2023: Tinubu Ya Nuna Bajintarsa Ta Rawar Da Ba A Saba Gani Ba Yayin Da APC Ta Kaddamar Da Kamfen A Filato

2023: Tinubu Ya Nuna Bajintarsa Ta Rawar Da Ba A Saba Gani Ba Yayin Da APC Ta Kaddamar Da Kamfen A Filato

  • Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress APC, ya taka rawa a wurin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyarsa a Jos
  • Dandazon masoya da magoya bayan mai fatan zama shugaban kasar sun masa maraba ta girma yayin da ya iso filin wasanni na Rwang Pam tare da abokin takararsa
  • Bisa irin tarba da maraba da dandazon mutanen suka masa, Bola Tinubu ya taka rawa yayin da sautin waka ke tashi a wurin taron

Jos, Plateau - Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ta kaddamar da yakin neman zabenta a Jos, babban birnin jihar Plateau, a ranar Talata, 15 ga watan Nuwamba.

Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar mai mulki da abokin takararsa, Kashim Shettima, sun isa filin motsa jiki na Rwang Pam kafin zuwar Shugaba Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Kamfen Tinubu: Gwamna ya fadi dalilin da yasa APC ta fara kamfen dinta a jihar Filato

Bola Tinubu
2023: Tinubu Ya Nuna Bajintarsa Ta Rawar Da Ba A Saba Gani Ba Yayin Da APC Ta Kaddamar Da Kamfen A Filato. Hoto: Hoto: Qudus Akanbi Eleyi of Lagos
Asali: Twitter

Tinubu ya nuna bajintarsa ta rawa a yayin da APC ke kaddamar da kamfen a Filato

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bisa alamu mai fatan zama shugaban kasar ya ji dadin irin tarbar da magoya bayansa suka masa yayin da ya iso.

Abin da ke faruwa da kamfen din takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, Remi Tinubu

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya nuna bajintarsa na rawa a wani bidiyo da shafin Tinubu/Shettima Media Support ta wallafa a Tuwita.

Tawagar watsa labaran ta yi wa bidiyoyin lakabi da:

"Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima sun iso filin wasanni na Rwang Pam don kaddamar da kamfenin din APC."

Dan takarar shugaban kasar mai shekara 70 ya yi wani motsi da hannunsa da yatsunsa yayin da ya ke taka rawa ga wakar da ake yi a wurin.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Gwamnan Arewa Mai Ƙarfin Iko Ya Bada Hutun Aiki Yayin Da Buhari, Tinubu Suke Ƙaddamar Da Kamfen Din APC

2023: Gwamnan Arewa Mai Ƙarfin Iko Ya Bada Hutun Aiki Yayin Da Buhari, Tinubu Suke Ƙaddamar Da Kamfen Din APC

A wani rahoto, Simon Lalong, gwamnan Filato, ya ayyana ranar Talata, 15 ga watan Nuwamba a matsayin ranar hutu a dukkan jihar saboda ziyarar Shugaba Muhammadu Buhari, Bola Tinubu da wasu shugabannin jam'iyyar APC.

Hakan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan labarai na jihar, Dan Manjang, da aka fitar a ranar Litinin 14 ga watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel