Zan Yi Kokarin Yadda Ba Zan Je Kasar Waje Neman Magani Ba a Matsayina Na Shugaban Kasa, Rabiu Kwankwaso

Zan Yi Kokarin Yadda Ba Zan Je Kasar Waje Neman Magani Ba a Matsayina Na Shugaban Kasa, Rabiu Kwankwaso

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP ya bayyana manufofinsa idan ya gaji shugaba Buhari a zaben 2023
  • Kwankwaso ya ce ba zai ke tafiya kasashen waje neman magani ba, domin zai inganta fannin kiwon lafiya a kasar nan
  • Wani dan takara kuwa cewa, ya kamata a ba mata dama su mulki Najeriya kasancewar maza sun dade suna tafiyar da ragamar kasar

Najeriya - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa ta yadda ba zai tafi kasar waje jinya ba idan aka zabe shi a 2023.

Ya bayana hakan ne a tattanawar baje kolin ra'ayoyin siyasa da Channels Tv ta gabatar a daren Lahadi 13 ga watan Nuwamba.

Yayin da aka tambaye shi game da fannin lafiya idan ya gaji Buhari, Kwankwaso ya ce:

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Akwai Kudi Dankam a Najeriya, Ba Zamu yi Rance Don Biyan Albashi ba

"Zan yi duk wani kokarin da zan iya wajen ganin ban fita ba [waje] don neman magani."
Kwankwaso ya ce ba zai ke tafiya waje neman magani ba
Zan Yi Kokarin Yadda Ba Zan Je Kasar Waje Neman Magani Ba a Matsayina Na Shugaban Kasa, Rabiu Kwankwaso | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Zan habaka fannin ilimin kiwon lafiya, na samar da kayan aiki, inji Kwankwaso

Kwankwaso ya ba da misali da irin ayyukan da ya yi a jihar Kano, inda yace da yake gwamna ya mai da hankali ne ga ilimi da kiwon lafiya, kuma haka zai yi idan ya gaji Buhari, Daily Trust ta ruwaito.

Hakazalika, ya ce gwamnatinsa za ta siyo kayan aiki na zamani ga asibitoci tare da ba mata guraben karatun zama likitoci a kasar nan.

Kwankwaso ya yi alkawarin inganta fannin lafiya ta yadda likitocin da suka bar Najeriya ma za su dawo don aiki a kasar.

Zan mai da hankali ga fannin ilimi

Tsohon gwamnan na Kano ya kuma bayyana cewa, babban abin da gwamnatinsa za ta mayar da hankali akai shine ilimi, tare da cewa za a samar kaso mai tsoka ga ci gaban fannin, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Ku yi hakuri: Gwamnan da ya muzanta Fulani ya kira su 'yan ta'adda ya nemi gafararsu

Da yake bayyana damuwa game da yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar nan, Kwankwaso ya ce, zai gina karin makarantu masu inganci a Najeriya don kiyaye goben yara.

Ya kuma yi alkawarin yakar rashawa da cin hanci, inda yace zai zuba hannun jari a fannin habaka masana'atu don inganta tattalin arzikin kasa.

Daga karshe ya yi watsi da maganar da ake cewa ya tsufa, kuma gashi kalubalen Najeriya na da matukar girma ga duk wanda ya gaji Buhari.

A bangare guda, dan takarar shugaban kas ana jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore ya ce ya kamata a ba mata damar mulkin kasar nan.

A cewarsa, mata sun fi yawa a Najeriya, amma sam ba a yi musu adalci.

Ya shawarci mata su tashi tsaye domin ganin sun tabbatar karbe ragamar kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel