Gwamna Ortom Ya Nemi Afuwar Fulani Kan Muzanta Su da Ya Yi, Ya Ce Ba da Nufi Ya Yi Ba

Gwamna Ortom Ya Nemi Afuwar Fulani Kan Muzanta Su da Ya Yi, Ya Ce Ba da Nufi Ya Yi Ba

  • Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya yi karin haske game da maganar da aka ce ya yi ta muzanta Fulani a kasar nan
  • Ortom ya ce ba zai goyi bayan Bafulatani ya zama shugaban kasa ba a Najeriya kasancewar kabila Fulani 'yan ta'adda ne
  • Ortom da gwamnonin Kudu na ci gaba da bayyana adawarsu ga tafiyar dan takararsu na shugaban kasa a jam'iyyar PDP

Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Benue, Dr Samuel Ortom ya nemi afuwar 'yan Najeriya da watakila suka ji ba dadi game da maganar da ya yi a baya na cewa ba zai goyi bayan Bafulatani ya gaji Buhari ba.

Ortom ya bayyana neman afuwar ne a jihar Bauchi ranar Laraba yayin da yake amsa tambayoyin 'yan jarida lokacin da yake tare da gwamnonin 'yan uwansa na tawagar G-5 masu adawa da takarar Atiku, Tribune Online ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Atiku Yana Da Tambayoyi Da Zai Amsa Kan Alakarsa Da Yan Ta'adda, In Ji Fani-Kayode

Idan baku manta ba, a martaninsa bisa kashe-kashen da suka faru a jiharsa daga wasu 'yan bindiga, gwamnan ya ce ba zai goyi bayan Bafulatani ya zama shugaban kasa a Najeriya ba.

Ortom ya ba Fulani hakuri kan batanci da ya yi musu
Gwamna Ortom Ya Nemi Afuwar Fulani Kan Muzanta Su da Ya Yi, Ya Ce Ba da Nufi Ya Yi Ba | Hoto: Leadershup News
Asali: Facebook

Wannan martani na Ortom ya jawo cece-kuce a tsakanin 'yan Najeriya, inda aka zargi gwamnan da nuna kin jinin wata kabila a kasar nan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ba abin da nake nufi ba aka yada

Da yake karin haske a jihar Bauchi kan maganarsa, Ortom ya ce:

"Ina son na bayyana cewa, ba abin da nake nufi ba kenan lokacin da aka dauki ina fadin haka."

Daga nan ya ce duk wanda ya ji haushi ya yi hakur, bai yi da nufi ba.

Rikicin G-5 da Atiku

Gwamna Ortom dai ba yanzu ya fara nuna kin jinin Fulani ba, ya sha nuna adawarsa ga gwamnatin Buhari tare da alakanta shugaban kasan da ayyukan ta'addanci a kasar nan.

Kara karanta wannan

Bacin rana: Kotu ta daure mai gadi a jihar Arewa bisa laifin barci a bakin aiki

A wannan karon, ya hada kai da gwamnonin Kudu domin nuna adawa da tafiyar Atiku matukar PDP bata tsige shugabanta ba, Sanata Iyochia Ayu.

A baya-bayan nan ya kuma bayyana cewa, duk mai goyon bayan Atiku to ya zama makiyinsa, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

A gefe guda, yayin da gwamnonin G-5 ke kan ziyara a jihar Bauchi, Atiku ya tafi Maiduguri domin gudanar da kamfen.

Rahotannin da muke samu sun bayyana yadda aka farmaki tawagar dan takarar, jama'arsa da dama sun jikkata.

Hakazalika, motoci da dama sun lalace yayin da tsageru suka farfasa komai da ke wurin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel