Akwai Kudi Dankare a Kasar nan, Ba Zamu Yi Rance Don Biyan Albashi ba, Kwankwaso

Akwai Kudi Dankare a Kasar nan, Ba Zamu Yi Rance Don Biyan Albashi ba, Kwankwaso

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ‘dan takarar kujerar shugabancin kasa a jam’iyyar NNPP, ya sanar da cewa akwai kudi dankare a kasar nan fiye da misali
  • Kwankwaso ya musanta ikirarin da ake yi na cewa tattalin arzikin Najeriya yayi kasa inda yace akwai kudin kula da kowanne ‘dan kasar Najeriya
  • Ya sanar da cewa idan ya samu shugabancin kasa, zai biya dukkan basukan da ake bin Najeriya kamar yadda yayi a jihar Kano sannan bai karbo bashi ya biya albashi ba

FCT, Abuja - ‘Dan takarar kujerar shugabancin kasa a karkashin New Nigerian People’s Party, NNPP, Rabiu Kwankwaso, yace Najeriya tana da isassun kudi da zata kula da dukkan ‘yan kasarta.

Sanata Rabiu Kwankwaso
Akwai Kudi Dankare a Kasar nan, Ba Zamu Yi Rance Don Biyan Albashi ba, Kwankwaso. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Ya sanar da hakan ne yayin ansa tambayoyi kan rancen kudin da yake mayar da tattalin arzikin kasar nan baya a cikin shekarun nan, a yayin taron da Channels TV ta shirya a Abuja da yammacin Lahadi.

Kara karanta wannan

Idan ya gaji Buhari: Kwankwaso ya magantu kan ko zai ke tafiya kasar waje neman magani

Mun biya dukkan basukan Kano, ba mu ranto wasu ba, Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano din wanda yace ya biya dukkan basukan da ya samu a jihar Kano yayin da yake gwamna kuma bai yi aron kudin ba, ya buga kirji inda yace hakan ce zata faru a matakin tarayya idan ya zama shugaban kasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yace:

“Akwai kudI mai yawa a kasar nan, duk wanda yace babu kudi sai dai bai sani ba ko kuma yana son rufawa. Akwai isasshen kudi da za a kula da kowa a kasar nan. Mun yi a Kano tsakanin 1999 zuwa 2003.

“Mun tarar da bashi mai yawa, mun biya bayan Shekaru takwas. Da na koma na sake tarar da bashin miliyoyin daloli kuma mun biya kafin in bar kujerar a 2015.

“Ina batun ranto kudi daga bankuna ko jama’a, ba mu taba arowa ba. Don haka na yarda cewa za a iya yin hakan a matakin tarayya.

Kara karanta wannan

Muna sane: IGP ya fadi matakin da 'yan sanda ke dauka bisa harin da aka kai kan tawagar Atiku

“Ban ce ba zan ranto kudi ba amma idan akwai muhimman abubuwa da za a yi da su ba wai a ranto a biya albashi ba, a yi manyan ayyuka da sauransu. Na yarda cewa akwai kudi fiye da misali a kasar nan da za a yi hakan.”

Zan nemi masu bin Najeriya bashi da su daga mana kafa, Kwankwaso

Channels TV ta rahoto cewa, Kwankwaso ya kara da cewa idan aka zabe shi ya zama shugaban kasa zai sasanta da masu bin Najeriya bashi da su daga kafa kan lokacin biyan ta yadda gwamnati zata samu kudin kula da wasu abubuwa.

“Halin da ake fada mana a yanzu shi ne, duk abinda ake samu a kasar nan baya isar mu balle a biya basuka. Yanzu batun shi ne, duk wata gwamnati da ta san abinda take yi tun daga ranar farko zata zauna da dukkan mutane, masu bin bashin kuma ta ga yanda zasu iya canza lokacin biyan.

Kara karanta wannan

2023: Kwankwaso Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Wa Kungiyar IPOB Idan Ya Zama Shugaban Kasa

“Ba zai yuwu ku tattara dukkan kudinsu ba kuma ku dinga biyan ruwan bashi ga masu bin bashi. Dole ya kamata a ce akwai wani yarjejeniya da za a baku sarari ta yadda zaku dinga kawo ababen arziki da suka dace da kasar ku kuma ya ciyar da ita gaba.”

- Yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel