Mun Karbi Tsohon Shugaban PDP da Mambobi 40,575 Zuwa APC, Kakakin Majalisar Kaduna

Mun Karbi Tsohon Shugaban PDP da Mambobi 40,575 Zuwa APC, Kakakin Majalisar Kaduna

  • Tsohon shugaban PDP, jiga-jigai da mambobin jam'iyyu sama da 40,000 sun koma APC a yankin Igabi, jihar Kaduna
  • Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Hon. Zailani, ya rokesu da su tabbata yan takarar APC sun samu nasara a 2023
  • A cewarsa, mutanen sun zabi shiga APC ne saboda dumbin ayyukan Alherin da gwamnati ta zuba musu

Kaduna - Shugaban ƙungiyar kakakin majalisun jihohi 19 na arewacin Najeriya kuma kakakin majalisar dokokin Kaduna, Rt. Hon. Ibrahim Yusuf Zailani, yace APC ta karbi dubbanin masu sauya sheka.

A Wani rubutu da ya saki a shafinsa na Facebook, Zailani yace mambobi 40,575 daga jam'iyyar PDP da wasu jam'iyyun siyasa sun rungumi APC a yankin ƙaramar hukumar Igabi, jihar Kaduna.

Kakakin Majalisar Kaduna, Yusuf Zailani.
Mun Karbi Tsohon Shugaban PDP da Mambobi 40,575 Zuwa APC, Kakakin Majalisar Kaduna Hoto: Speaker Zailani/facebook
Asali: Facebook

Yace daga cikin jiga-jigan da suka sauya sheƙa zuwa APC har da tsohon shugaban PDP a ƙaramar hukumar Igabi, Honorabul Jafaru Murtala. A cewarsa sun ɓinne PDP a yankin.

Kara karanta wannan

Da Dumi: PDP Tayi Nasara Jam'iyyar APC Ba Tada Yan Takara a Kujerun Majalisar Rivers 16, Kotu ta Yanke hukunci

Haka zalika Legit.ng Hausa ta gano cewa daga ciki akwai tsofaffin Kansilolin PDP a yankin ƙaramar hukumar da wasu jiga-jigan tsagin adawa, duka sun koma inuwar APC.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake karɓan masu sauya shekar, mafi yawa matasa da mata a Kasuwar duniya dake Titin Kaduna-Zariya, Honorabul Zailani yace gwamnatin APC ta yi abin azo a gani ga mutanen Igabi.

Shugaban majalisar dokokin ya ƙara da cewa zaɓen 2023 mai zuwa zai zama wani lokaci ne na saka wa APC bisa romon demokuraɗiyyar da ta shayar da mutane.

Yace wasu daga cikin masu sauya shekan sun rike muƙamai a gwamnatin PDP amma suka ga APC ta fi taka muhimmiyar rawa a rayuwarsu kuma ta aiwatar da ayyukan da zasu amfani al'umma.

Wajibi mu zaɓi Tinubu a 2023 - Hon Zailani

Bugu da ƙari, Zailani yace goyon bayan ɗan takarar shugaban ƙasa a APC, Bola Tiɓubu, ya zama wajibi saboda mai ƙaunar arewa ne domin goyon bayansa ne ya kawo shugaban kasa Buhari.

Kara karanta wannan

Dattawan Yarbawa Sun Tsaida 'Dan Takaransu Tsakanin Tinubu, Atiku, Obi da Kwankwaso

"Karmu yarda da masu cewa naka naka ne mu zaɓi namu, bai kamata mu buga siyasar yanki a 2023 ba, ina rokon ku zaɓi 'yan takarar APC tun daga sama har ƙasa," inji shi.

Legit.ng Hausa ta zanta da wani mazaunin Daura Road, Rigasa, karamar hukumar Igabi a Kaduna, Aliyu Abdulhamid, mamban APC, yace wannan ma somin taɓi ne domin basu san ana mulki ba sai da Malam ya zo.

Ɗan siyasan yace mutanen Rigasa sun ga canji a mulkin APC, "A baya watsi ake da mu saboda kuri'unmu mafi yawa na jam'iyyar adawa ne, zuwan gwamnatin APC mun ga ayyuka."

"Wannan sauya sheka ba abun mamaki bane domin ko baka siyasa zaka shiga yanzu domin a shekara 7 baya ne muka san cewa gwamnati ta san da zamanmu."

Sai dai wani mazaunin yankin, Kabiru Tanibu, yabo ya yi ga kakakin majalisar dokokin Kaduna, a cewarsa ya jima yana wakiltar Igabi ta yamma a wannan karon sun ga ɗumbin ayyuka.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar APC Ta Samu Gagarumin Goyon Baya, Jiga-Jigan PDP Sama da 300 Sun Koma Bayan Tinubu

A wani labarin kuma Rabiu Musa Kwankwaso yace ya so jam'iyyar APC da PDP su tsayar da gwamna Umahi da Wike a takarar shugaban kasan 2023

Da yake jawabi bayan kaddamar da Ofishin NNPP a Enugu, Kwankwaso yace gwamna Umahi na jiha% ya tafka kuskure da ya zabi shiga jam'iyyar APC.

Yace rashin tsayar da yan takara masu nagarta da manyan jam'iyyu biyu suka yi ne zai ƙara share masa fagen ɗarewa mulkin Najeriya cikin sauki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel