Kotu Ta Soke Takarar Masu Neman Kujerar Majalisar Karkashin APC 16

Kotu Ta Soke Takarar Masu Neman Kujerar Majalisar Karkashin APC 16

  • Jam'iyyar APC ta sake shiga sabon tasku a jihar Rivers kamar yadda aka yi a zaben 2019
  • Kotu ta yanke hukuncin cewa jam'iyyar ba za tsayar da yan takara a wasu mazabun majalisa 16 ba
  • Jam'iyyar APC karkashin Rotimi Amaechi a jihar Rivers ta gaza dinke barakarta tun shekarar 2019 har yanzu

PortHarcourt - Wata babbar kotun tarayya dake Fatakwal, jihar Rivers a ranar Juma'a ta soke takarar mutum 16 masu neman kujerar yan majalisu a majalisar dokokin jihar Rivers a 2023.

Yan takaran dukkansu yan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ne.

Za ku tuna cewa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta shigar da hukumar INEC da yan takaran APC 33 kotu inda ta bukaci a soke dukkan zabukan fidda gwanin APC saboda jami'an INEC basu halarcesu ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Fitittiki Emmanuel Bwacha Daga Kujerar Sanata

Alkalin kotun, Mohammed Turaki Adamu, ya gaskata maganar PDP kuma ya fitittiki yan takaran, rahoton Leadership.

Mazabun da APC ba tada yan takara a zaben 2023 yanzu sun hada da Andoni, Etche I da II, Tai, Gokana, Oyigbo, Eleme, Port Harcourt I, II da III, Khana I da II Okrika, Ahoada West da Obio/Akpor I/II.

APC RIvers
Kotu Ta Soke Takarar Masu Neman Kujerar Majalisar Karkashin APC 16 Hoto: APC
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Martanin APC

Shugabannin jam'iyyar APC na jihar sun yi kira ga mambobinsu da mabiyansu su kwantar da hankulansu kuma kada su damu da hukuncin kotun, riwayar Nigerian Info.

Kakakin Kwamitin yakin neman zaben jihar Sogbeye Eli, a jawabin da ya fitar a Port Harcourt ranar Juma'a ya ce jam'iyyar za ta daukaka kara.

A cewar jawabin:

"Kwamitin kamfe na kira ga mambobin jam'iyyarmu da miliyoyin mutan jihar Rivers masu goyon bayan yan takaranmu a wadannan mazabu cewa kada su fidda tsamanni saboda mun zamu daukaka kara."

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP Da Suka Bayar Da Sharudda A Bainar Jama'a Kafin Yi Wa Atiku Aiki A Jihohinsu

"Makiya demokradiyya a jiharmu masu tsoron bugawa da mu ranar zabe na kokarin karya mana lago amma basu isa ba.'
"Zamu yi takara a zabukan nan masu zuwa kuma muyi nasara bayan an yi watsi da wannan hukunci."

Dan takaran Gwamnan jihar Ribas na jam’iyyar APC ya gamu da cikas

A ranar 24 ga watan Nuwamban 2022, kotu za ta yanke hukunci kan Tonye Cole dan takarar gwamna jihar Ribas a zabe mai zuwa.

A ranar Litinin, an shigar da Tonye Cole da nufin a hana shi neman zama Gwamnan jihar Ribas a karkashin jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel