Jiga-Jigan PDP Sama da 300 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a jihar Ondo

Jiga-Jigan PDP Sama da 300 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a jihar Ondo

  • Watanni kalilan gabanin babban zaɓen 2023, jam'iyyar APC ta samu karin goyon baya a jihar Ondo
  • Wasu kusoshin jam'iyyar PDP mai adawa sama da 300 suka sauya sheka zuwa APC a yankin karamar hukumar Idanre
  • Shugaban APC a jihar Ondo, Ade Adetimehin, yace wannan ba karamar nasara bace kuma su ɗauka an zama ɗaya

Ondo - Aƙalla kusoshin jam'iyyar PDP 300 ne suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki a yankin ƙaramar hukumar Idanre jihar Ondo, makonni kaɗan gabanin zaɓen 2023.

Kakakin jam'iyyar APC, Mr Steve Otaloro, shi ne tabbatar da lamarin ranar Litinin, yace mutanen sune tushen siyasa dake haɗa kan masu kaɗa kuri'a daga sassa daban-daban na karamar hukumar.

PDP zuwa APC.
Jiga-Jigan PDP Sama da 300 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a jihar Ondo Hoto: punchng
Asali: UGC

Jaridar Punch ta tattaro cewa a wurin taron tarban sabbin masu sauya shekar, shugaban APC na jihar Ondo, Ade Adetimehin, ya yaba wa mutanen bisa kwarin guiwar haɗa kai da jam'iyyar nasara.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa a APC, Wani Babban Jigo da Wasu Shugabanni Sun Ayyana Goyom Baya Ga Ɗan Takarar PDP a 2023

Ya kuma tabbatar musu da cewa babu ko ɗaya daga cikinsu da za'a nuna masa shi sabon shigowa ne, APC zata rungumesu daidai da kowane mamba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mista Adetimehin ya roki su yi amfani da basirar da Allah ya basu a siyasa wajen aiki ba dare ba rana domin nasarar dukkan 'yan takarar APC a zaɓen 2023 mai zuwa.

A ruwayar Vanguard shugaban APC yace:

"Taron yau na daban ne, kowa na nan wurin, yan siyasa ne da aka gwada aka gani, daga cikinsu akwai tsaffin shugabannin gunduma Kansiloli da zababbun shugabanni a matakin karamar hukuma, har da kakakin tsohon ɗan takara."
"Idan mutum 300 suka bar jam'iyya ba karamin abu bane kuma daga tushe. Idanre cike take da wayayyun mutane, ina baku tabbacin daga yanzu kowane lokaci, APC zata yi nasarar zaɓe a Idanre."

Kara karanta wannan

2023: Ƙarin Ciwan Kai Ga Atiku, Jam'iyyar APC Ta Ƙara Samun Gagarumin Goyon Baya Daga Wasu Jiga-Jigan PDP

"Saboda haka ina kira ga kowanen ku ya koma yankinsa ya haɗa kan mutane saboda muna son ya zama dole a kanmu dukkan yan takarar APC su ci zaɓe."

Ayo Fayose ya gargaɗi PDP kan abinda ke tunkarowa

A wani labarin kuma Tsohon Gwamnan PDP Ya Hango Babbar Matsala Ga PDP, Atiku Gabanin 2023

Tsohon gwamnan jihar Ekiti dake goyon bayan tsagin Wike ya yi hasashen cewa akwai babban rikici mai muni dake tunkaro PDP.

Ayodele Fayose, yace yana ba masu ruwa da tsaki shawarin su ɗauki matakai tun gabanin abun ya ci karfinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel