Dattawan Yarbawa Sun Tsaida 'Dan Takaransu Tsakanin Tinubu, Atiku, Obi da Kwankwaso

Dattawan Yarbawa Sun Tsaida 'Dan Takaransu Tsakanin Tinubu, Atiku, Obi da Kwankwaso

  • Manya da dattawan da suka fito daga kasar Yarbawa su na kara nuna za su goyi bayan Asiwaju Bola Tinubu
  • Kungiyoyin magoya baya su na sa ran Sarakuna, Mogaji, da Baale kusan 10, 00 su marawa APC baya a 2023
  • Shugabannin SWAGA sun kwallafa rai a kan kuri’u miliyan 15 daga jihohin Kudu maso yammacin Najeriya

Oyo - Dattawan kasar Yarbawa sun tabbatar da goyon bayansu Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasar da za ayi a farkon shekarar badi.

Manyan Yarbawan sun yi kira ga ‘Yan Najeriya, musamman ‘yan kabilarsu da su zabi Bola Tinubu. Jaridar The Nation ta fitar da wannan rahoto a jiya.

Kungiyar Yoruba Council of Elders ta dattawan kabilar, ta fadakar da mutanenta cewa su guji maimaita kuskuren da iyayensu suka yi a zaben 1963.

Kara karanta wannan

Tinubu, Atiku Sun Gagara Halartar Taron ‘Yan Takara, Kwankwaso, Obi Sun Yi Kasuwa

Ma’ajin kungiyar, Aremu Akindele yace a 1963, an samu wasu da suka bi bayan Nnamdi Azikwe, a karshe suka tafi neman gafarar Obafemi Awolowo.

Muna tare da Afenifere - YCE

A jawabin kungiyar, ta nuna tana tare da Pa Fasoranti da Farfesa Akintoye da suka dauki matsayar cewa ‘dan takaran APC shi ne zabin Yarbawa a 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Aremu Akindele yake cewa a 1979, haka aka yi da Alhaji Waziri Ibrahim ya bar NPP bayan ya fahimci Ibo sun mamaye jam’iyyarsa, ya kafa GNPP.

Bola Tinubu
Bola Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Mogaji da Baales sun ce sai Tinubu

Ana haka ne sai rahoto ya fito daga Premium Times cewa manyan dangogin Yarbawa wadanda aka fi sani da Mogaji, sun bi Bola Tinubu da APC.

Mogaji, Baales da sauran kungiyoyi irinsu Agbekoya na reshen Ibadan sun yi wa ‘dan takaran mubaya’a a wani taro da aka yi a ranar Asabar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Ana Zargin Gwamnan PDP da Ya Raba Jiha da Atiku Zai Yi wa Tinubu Aiki a Zaben 2023

Hukumar dillacin labarai na kasa tace an yi taron ne a otel din Ilaji Hotels & Sports Resort.

Kungiyoyin Agbekoya, da O’dua Peoples Congress (OPC) na bangaren Fasehun, da Irorun O’dua da 'Yan Akwa Ibom da ke zaune a Oyo sun yi mubaya'a.

Shugaban kungiyar SWAGA Oyetunde Ojo ya nuna Baales, Mogajis, da Oba kimanin 10, 000 sun sa hannu domin tabbatar da cewa za a goyi bayan Tinubu.

Bosun Oladele yace Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yana harin kuri’u miliyan 15 daga jihohin da suke yanin Kudu maso yammacin Najeriya a babban zabe.

Matsala a PDP

Rahotanni na nuna an sake samun Gwamnan PDP da yake neman raba gari da Atiku Abubakar, ya na zargin 'dan takaran bai goyon bayan da tazarcen shi.

A halin yanzu PDP tana cikin matsala domin Iyorchia Ayu yana rigima da Nyesom Wike da wasu Gwamnonin PDP da ke cin dunduniyar Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Sai Ta An yi Addu'a, Ubangiji Bai Fada Min Za'a Yi Zabe A 2023 Ba, Fasto Enoch Adeboye

Asali: Legit.ng

Online view pixel