Ba Karamin Kuskure Umahi Ya Tafka Ba Na Sauya Sheka Zuwa APC, Kwankwaso

Ba Karamin Kuskure Umahi Ya Tafka Ba Na Sauya Sheka Zuwa APC, Kwankwaso

  • Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso yace akwai wasu mutum biyu da ya so su samu tikitin shugaban kasa a APC da PDP
  • Mai neman kujera lamba ɗaya a Najeriya karkashin NNPP yace gwamna Umahi ya yi gaggawar shiga jam'iyyar APC
  • Kwankwaso ya buɗe sabon Ofishin jam'iyya mai kayan marmari a jihar Ebonyi yau Laraba

Ebonyi - Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso yace gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya yi gaggauwar sauya sheƙa zuwa APC.

Alhaji Kwankwaso ya yi wannan furuci ne yayin da ya kai ziyara Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi ranar Laraba a wani bangaren yawon neman kuri'un jama'a a sassan ƙasar nan.

Sanata Kwankwaso.
Ba Karamin Kuskure Umahi Ya Tafka Ba Na Sauya Sheka Zuwa APC, Kwankwaso Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Asali: Twitter

A cewarsa, Najeriya na bukatar mutum mai kwarewa, gogagge kuma mai kuzarin da zai sauya ƙasar nan. Ya faɗi sunan mutum biyu ya so su zama shugaban kasa, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Kamata Ya Yi Ace Muna Tare": Abinda Gwamnan Bauchi Ya Faɗa Wa Wike da 'Yan G5

Kwankwaso ya kuma kai ziyarar gaisuwa ga gwamnan jihar Ebonyi a masaukin shugaban ƙasa da ke tsohon gidan gwamnati, Abakaliki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Har ila yau, mai neman zama shugaban ƙasa a NNPP wanda ya samu rakiyar dattijon ƙasa, Buba Galadima ya buɗe sabon Ofishin jam'iyyarsa a kusa da babban Titin kasuwa, Abakaliki.

Tsohon gwamnan jihar Kano ya maimaita cewa shi da gwamna Umahi a wancan lokacin sun fusata da PDP kuma suka yanke cewa zaau tattara su barta saboda matsalolin da suka baibaye jam'iyyar.

"Muka kafa APC kuma muka karɓi shugabancin ƙasa a 2015, bisa rashin sa'a sai ya zama mun yi gudun gara mun aukawa zago, abinda muka gudo a PDP ya fi muni a APC," inji shi.

Wane mutane Kwankwaso ya so su karɓi mulkin Najeriya?

Kwankwaso yace jam'iyyar APC ta damƙa tikitin takarar shugaban ƙasa hannun wanda bai dace ba, inda ya kara da bayanin cewa zai yi farin ciki idan Gwamna Umahi ko Wike ne suka zama shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

2023: Wasu Daga Cikin Gwamnonin Tsagin Wike Na Shirin Yaudararsa, Zasu Koma Bayan Atiku

"NNPP ce jam'iyya mai nasara a arewa babu ɓurɓushin APC a zuƙatan yan arewa domin ta kunyata mutane. Mun ji daɗi yan takara masu karfi basu samu tikitin jam'iyyunsu ba."

A wani labarin kuma An fara guna-Guni kan rashin halartar Ayu a wurin kamfen Atiku a Maiduguri, Kakakin sa ya bayyana dalili

A wata sanarwa da babban mai taimaka wa shugaban PDP na ƙasa kan harkokin Midiya da sadarwa, Simon Imobo-Tswam, yace wasu muhimman taruka ne suka rike Ayu.

Riigingimu sun hana PDP zaman lafiya yayin da Wike da yan tawagarsa ke neman a yi wa yankin kudu adalci a tsakanin manyan muƙamai biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel