Rikicin PDP: Ayu, Tambuwal da Sule Lamido Sun Gana Da Gwamnan Bauchi

Rikicin PDP: Ayu, Tambuwal da Sule Lamido Sun Gana Da Gwamnan Bauchi

  • Manyan jiga-jigan jam’iyyar Peoples Democratic Party sun gana da gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed a ranar Asabar
  • Shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu, gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal da tsohon gwamnan jihar Jigawa na cikin wadanda suka yi ganawar cikin sirri
  • Daga cikin abubuwan da suka tattauna harda batutuwan da suka addabi jam’iyyar gabannin babban zaben 2023

Bauchi - Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya isa jihar Bauchi a ranar Asabar domin ganawa da Gwamna Bala Mohammed.

Ayu ya samu rakiyar darakta janar na kungiyar kamfen din takarar shugaban kasa na PDP, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto da kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, PM News ta rahoto.

Jiga-jigan PDP
Jiga-jigan PDP sun gana a Bauchi Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Tawagar sun isa Bauchi da yamma sannan suka yi wata ganawar sirri tare da mai masaukinsu, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

2023: Wike Da Wasu Gwamnoni 4 Da Suke Fushi Da PDP Sun Hada Kai Da Tinubu, Ortom Ya Rungumi Peter Obi

Da yake jawabi jim kadan bayan ganawar, Ayu ya bayyana Mohammed a matsayin daya daga cikin manyan masu ruwa da tsaki na kasa wadanda suka bayar da gudunmawa wajen ci gaban jam'iyyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Mun zo nan ne don sanar da kai wasu ci gaba da ke gudana a jam'iyyar, sannan mu ji shawararka mai cike da hikima saboda kai ba gwamnan Bauchi bane kawai, kai shugaba ne a kasar nan.
"Kana da kwarewa a duk wuraren da kayi aiki, kuma muna bukatar mutane irinka a wannan kamfen din, daga lokaci zuwa lokaci ya zama dole mu dunga zagayoqa, mu tuntuba sannan mu sanar maka da wasu abubuwa."

Da yake martani, Mohammed ya bayyana cewa shi din dan jam'iyya ne mai biyayya kuma da yarda da ita, yana mai cewa:

"Mun jingina da bangon jam'iyyar wajen zama abun da muka zama.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Makusantan Amaechi Da Suka Fice Daga APC Suka Koma Wurin Wike A PDP Ta Jihar Ribas

"Mun san cewa mun zo ne daga jam'iyyar ANPP, amma tabbass duk abun da muka zama sanadiyar wannan jam'iyyar ce.
"Mun tattauna lamuran da suka shafi jam'iyyar musamman a yankina a matsayin mataimakin shugaban kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa wanda ke kula da arewa."

Muhammed ya fada ma manema labarai cewa bakinsa sun zo ne dangane da wasu batutuwa da bai shafi jama'a ba.

Gwamnonin APC 5 Na Tattaunawa da Atiku Abubakar

A wani labarin, jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) ta ce gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) 5 na cikin tattaunawa da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar, Kola Ologbondiyan ne ya bayyana hakan a wata hira da jaridar Daily Independent, a ranar Alhamis, 3 ga watan Nuwamba.

Ya kuma bayyana cewa kudirin APC da dan takararta na shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu na ci daga rikicin da ke tsakanin Atiku da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ba zai cimma nasara ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnonin APC 5 Na Tattaunawa da Atiku Abubakar

Asali: Legit.ng

Online view pixel