2023: Jerin Makusantan Amaechi Da Suka Fice Daga APC Suka Koma Wurin Wike A PDP Ta Jihar Ribas

2023: Jerin Makusantan Amaechi Da Suka Fice Daga APC Suka Koma Wurin Wike A PDP Ta Jihar Ribas

  • Muhimmancin jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a siyasar jihar Rivers na fuskantar barazana mafi girma
  • Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, mai mulki a jihar na cigaba da mamaye siyasar jihar
  • Jam'iyyar ta PDP ta yi karfin da har tana kwace wasu manyan jiga-jigan APC gabanin zaben 2023

Rivers - Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, reshen jihar Rivers ta fara rasa jiga-jiganta a yayin da babban zaben 2023 ke karatowa.

Jihar da a baya jam'iyyar APC ne ke juya ta karkashin tsohon gwamna Rotimi Ameachi yanzu ta zama jam'iyyar ta rikice-rikice suka yi mata yawa.

Na hannun daman Amaechi
2023: Jerin Makusantan Amaechi Da Suka Fice Daga APC Suka Koma Wurin Wike A PDP Ta Jihar Ribas. Hoto: Photo: Chris Finebone, Ibim Semenitari, Princewill Dike.
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ko karfin ikon Ameachi daga gwamnatin tarayya bai isa dakile buwayar jam'iyyar PDP karkashin Gwamna Nyesom Wike ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnonin APC 5 Na Tattaunawa da Atiku Abubakar

Bugu da kari, APC tana cigaba da rasa jiga-jiganta da suke komawa PDP, wasunsu na hannun daman tsohon gwamna Rotimi Amaechi.

A wannan gajerun rubutun, Legit.ng za ta duba ga wasu na hannun daman tsohon gwamna Rotimi Ameachi da suka sauya sheka suka hada karfi da Gwamna Wike na PDP.

1. Barister Princewill Dike

Fitar Princewill Dike daga jam'iyyar APC da komawarsa jam'iyyar PDP ya bawa mutane da dama mamaki saboda an san yana daya daga cikin hadiman tsohon gwamna Amaechi na kut-da-kut.

Dike ya yi aiki a matsayin hadimi na musamman kan harkokin dalibai a karkashin gwamnatin Rotimi Amaechi.

Da aka tambaye shi dalilin da yasa ya fice daga APC ya koma PDP, ya ce:

"Jam'iyyar siyasa hanya ce ta samun karfi na siyasa. Da na lura APC ta jihar Rivers ta kama hanyar rugujewa, na fara kokawa. Sun rika min kallon mai mugun fata, kamar yadda yan Isra'ila suka yi wa Jeremiah.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Fitittiki Dan Takaran Gwamnanta A Jihar Ogun Na Jam'iyyar PDP

"Ban dena kokawa ba, amma na bada hanyoyin warware matsalar amma ba a kula ni ba. Ba a karbi shawara ta ba. Don haka, me zai sa in cigaba da kasancewa a jam'iyyar da ke kan hanyar rushewa in watsar da siyasa ta?".

2. Chris Finebone

Yin murabus din Chris Finebone daga APC shima ya girgiza mutane da dama.

Finebone ya yi aiki a matsayin sakataren watsa labarai na APC ta jihar Rivers.

Jam'iyyar PDP ta yi maraba da tsohon na hannun daman Amaechin kuma bayan wasu yan makonni an bashi mukami a gwamnatin Wike.

3. Ibim Semenitari

A wani yanayi mai ban mamaki, Gwamna Wike ya yi zawarcin Ibim Sementari, tsohuwar kwamishinan sadarwa karkashin Ameachi kuma yar tsohon mataimakin gwamna ga tsohon gwamna Peter Odili, Sir Gabriel Toby.

Ana sa ran Semenitari za ta taka muhimmin rawa wurin yakin neman zaben dan takarar gwamna na PDP a jihar Rivers, Siminialayi Fubara.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Atiku ya samu nakasu a Sokoto, manyan jiga-jigai sun koma APC

Abin Da Wike Ya Fada Wa Atiku A Sabuwar Ganawar Da Suka Yi Kan Rikicin PDP

A kokarin warware rikicin jam'iyyar PDP, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya sake ganawa da Gwamna Mr Nyesom Wike na Jihar Rivers.

Wata majiya da ta halarci taron ta shaidawa Daily Trust cewa wasu hadiminan bangarorin biyu sun halarci taron.

Asali: Legit.ng

Online view pixel