2023: Wike Da Wasu Gwamnoni 4 Da Suke Fushi Da PDP Sun Hada Kai Da Tinubu, Ortom Ya Rungumi Peter Obi

2023: Wike Da Wasu Gwamnoni 4 Da Suke Fushi Da PDP Sun Hada Kai Da Tinubu, Ortom Ya Rungumi Peter Obi

  • Atiku Abubakar zai rasa goyon bayan gwamnonin jam'iyyar PDP biyar a yunkurinsa na zama shugaban Najeriya
  • Gwamnoni hudu sun yanke shawarar hada kai da Asiwaju Ahmed Bola Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki
  • Yayin da shi kuma gwamna guda daya da ya rage an rahoto yana goyon bayan Peter Obi na Labour Party

FCT Abuja - Akwai yiwuwar gwamnoni hudu cikin biyar da ke fushi da jam'iyyar PDP sun dauki matakinsu na karshe kan dan takarar shugaban kasa da za su goyi baya a zaben 2023.

Gwamnonin hudun sune Nyesom Wike na jihar Ribas; Seyi Makinde na jihar Oyo; Okezie Ikpeazu na jihar Abia da Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu.

Atiku Abubakar
2023: Wike Da Wasu Gwamnoni 4 Da Suke Fushi Da PDP Sun Hada Kai Da Tinubu, Ortom Ya Rungumi Peter Obi. Hoto: Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar jaridar Daily Sun, sauran gwamnan daya da ke fushi da jam'iyyar, Samuel Ortom na jihar Benue ba dole ne ya bi sahun sauran gwamnonin hudu ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnonin APC 5 Na Tattaunawa da Atiku Abubakar

Fusatattun gwamnonin da suka janye kansu daga kwamitin yakin neman zabe na PDP, a cikin satin nan sun ce babu ja da baya kan bukatunsu.

A bangarensa, dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, ya ce fa tuni jirginsa ya bar tasha, kamar yadda aka rahoto.

Rahoton ya ce idan ba an samu wani canjin kurarren lokaci ba, gwamnonin hudu da aka ambata za su goyi bayan takarar shugaban kasa na Bola Ahmed Tinubu na APC.

Wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ta ce tunda gwamnonin sun gaza yin sulhu da Atiku, zabin da ya rage musu shine tsakanin Tinubu da Peter Obi na LP.

Majiyar ta ce bisa alamu Ortom shine bare cikin gwamnonin biyar, wanda ta yiwu ya goyi bayan Obi, yayin da sauran hudun za su goyi bayan Tinubu idan aka amince da sharrudansu.

Majiyar ta kara da cewa kuma Wike, Uguwanyi da Ikpeazu, suna neman a basu wasu mukamai a gwamnatin Tinubu idan ya ci zabe.

Kara karanta wannan

2023: Shugabannin PDP Sun Hargitse Bayan Wani Gwamna Ya Ayyana Goyon Bayan Tinubu a Fili

Wike da sauran gwamnonin 4 ba za su yi murabus daga PDP ba, Majiya

Ya ce duk da cewa ba za su yi murabus daga PDP ba saboda yan takararsu, amma za su yi wa APC aiki ta karkashin kasa.

Dan siyasan ya ce:

"Wike tuni ya fara aikin, da nadin dubban hadimai da ya yi, da ake fatan za su saka idanu a mazabu yayin zaben jihar Rivers.
"Wike da Atiku ba za su yi sulhu ba. Wike na bukatar ya goyi bayan wani dan takara kuma wanda ake tunani shine Tinubu. Suna ta haduwa. Wike ya fi yarda da Tinubu, don haka zai goyi bayan dan takarar na APC.
"Amma ya bada sharrudansu wadanda suna da wuya Tinubu ya cika. Muna tsammanin ganin hadin gwiwa, sai dai idan wani abu ya faru. Ugwuwanyi, Makinde da Ikpeazu suna tare da shi.
"Ka ga lokacin da mataimakin Makinde ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu a Akure, babban birnin jihar Oyo."

Kara karanta wannan

2023: Gaskiyar Abun da Ke Tsakanina Da Wike, Ortom da Sauran Jiga-Jigan PDP, Peter Obi Ya Fasa Kwai

A game da Ortom, majiyar ta ce:

"Ortom ya dauki mataki na daban a yanzu. Ba mu san ko hakan zai canja ba. Amma wannan shine abin da ke faruwa a yanzu. Tinubu yana samun nasara, yayin da Atiku ya makale yana tunanin kuri'un arewa za su taimake shi."

Zaben 2023: Mataimakiyar Kakakin APC Ya Bayyana Jihohin Arewa Da Obi Zai Iya Cin Zabe

Duba da kara karbuwa da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, LP, ke kara samu, jam'iyyar APC ta yi wani hasashe kan wasu abubuwa da ka iya faruwa a babban zaben 2023.

Mataimakiyar kakakin kungiyar kamfen din shugaban kasa na APC, Hannatu Musawa, wacce ta yi magana da The Punch a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba ta ce akwai yiwuwar Obi ya samu kuri'un wasu jihohin arewa da kowane dan takara ke bukata don cin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel