Mataimakiyar Shugabar LP Ta Rabu da Peter Obi, Ta Koma Goyon-Bayan Atiku Abubakar

Mataimakiyar Shugabar LP Ta Rabu da Peter Obi, Ta Koma Goyon-Bayan Atiku Abubakar

  • Mayoress Olubukola Olayinka za ta taya Atiku Abubakar da Dr. Ifeanyi Okowa kamfe a zaben 2023
  • Kafin ta ajiye kujerarta, Mayoress Olayinka ce mataimakiyar shugaban jam’iyyar Labour Party a Oyo
  • ‘Yar siyasar ta canza sheka zuwa Jam’iyyar PDP, tace Atiku Abubakar ne ‘dan takaran da ya fi dacewa

Oyo - Takarar Alhaji Atiku Abubakar da Dr. Ifeanyi Okowa a jam’iyyar PDP ta samu gagarumar kwarin gwiwa daga bangaren jam’iyyar adawa ta LP.

Vanguard ta fitar da rahoto cewa mataimakiyar shugaban jam’iyyar Labour Party a jihar Oyo, Mayoress Olubukola Olayinka ta canza shekar siyasa.

Mayoress Olubukola Olayinka da daruruwan mabiya da magoya bayanta da ke jam’iyyar hamayyar, za su marawa PDP baya a zabe mai zuwa.

Da take bayani a ranar Talata, Mayoress Olayinka ta shaidawa mutanenta za tayi kokarin ganin takarar shugaban kasar Atiku/Okowa ta kai labari.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Dare Gida Biyu a Jihar Arewa, Ta Dakatar da Ɗan Takarar Gwamna a 2023

Ka da a biyewa yaudarar 'yan siyasa

‘Yar siyasar tayi kira ga magoya baya da sauran jama’a suyi hattara da zakin bakin ‘yan siyasa, tace akwai masu neman mulki domin taba Baitul-mali.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A jawabinta, tsohuwar shugabar jam’iyyar ta LP ta soki gwamnatin APC mai-ci, wanda tace ta gaza.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar a Oyo Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Independent tace Mayoress Olayinka tayi suka a kan shugabannin LP na reshen jihar Oyo, ta kuma yabi Atiku mai neman takarar shugaban kasa a PDP.

"Atiku ya fi kowa cancanta"

"A matsayin wanda ya yi ritaya daga gidan Kwastam, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ne kadai ‘dan takarar da zai iya dawo da hadin-kai da martabar kasar nan.
Atiku bai taba ba kuma ba zai taba cin amanar mutanensa ba, akasin masu ihun ‘Emilokan’.

- Mayoress Olubukola Olayinka

Rikicin cikin gidan LP

Kara karanta wannan

Ka yi kadan: Gwamna Wike Ya Aikawa Shugaban Jam’iyyar PDP Sabon Raddi

Bayan wannan jawabi, jagorar ta bada sanarwar barin Labour Party tare da sauran jama'anta, dalilin canza shekar, tace shi ne rikici da ake tayi a jihar Oyo.

A cewarta, Alhaji Atiku Abubakar bai da kabilanci, saboda haka idan aka zabe shi a 2023, zai dunkula kan Najeriya, kuma ya farfado da tattalin arzikin kaa.

Kano: Babu zaman lafiya a APC

Bayan abin da ya faru tsakanin Alhassan Ado Doguwa da Murtala Sule Garo, an ji labari a yau cewa an sake yin wata arangama da kakakin APC na Kano.

Hon. Alhassan Ado Doguwa ya naushi Ahmad Aruwa a lokacin da ya zo gidansa. 'Dan majalisar ya kuma ja-kunnen wasu jagororin APC ta wayar salula.

Asali: Legit.ng

Online view pixel