Ka yi kadan: Gwamna Wike Ya Aikawa Shugaban Jam’iyyar PDP Sabon Raddi

Ka yi kadan: Gwamna Wike Ya Aikawa Shugaban Jam’iyyar PDP Sabon Raddi

  • Gwamna Nyesom Wike ya maida martani ga jawabin da aka ji shugaban jam’iyyar PDP na kasa ya yi
  • Iyorchia Ayu ya yi ikirarin zai iya hana mutum takara, amma Wike yace Ayu bai da wannan karfi a doka
  • Gwamnan ya kalubalanci shugaban jam’iyyar ya soke takarar wasu daga cikin ‘yan takaran PDP a Ribas

Rivers - Gwamna Nyesom Wike ya maida martani bayan shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu yace zai iya hana wasu shiga takara.

Daily Trust ta rahoto Mai girma Nyesom Wike yana mai kalubalantar Iyorchia Ayu ya hana wani ‘dan takaran jam’iyyar PDP shiga zabe a 2023.

Wike ya zanta da manema labarai a garin Fatakwal, yana yin raddi ga shugaban jam’iyyarsa.

A cewar Gwamnan, babu wanda yake kiran a sauke Ayu daga mukaminsa, sai dai ana neman ya yi murabus saboda Atiku Abubakar ya samu tikiti.

Kara karanta wannan

2023: Tsagin Gwamna Wike Sun Sake Yunkuro Wa, Sun Huro Sabuwar Wuta a Jam'iyyar PDP

Jawabin Gwamna Nyesom Wike

"Kalaman da suka fito daga bakin shugaban PDP na kasa na hana wani ‘dan takara shiga zabe, abin takaici ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babu wanda yace a tsige Sanata Iyorchia Ayu. A tsarin mulkinmu, akwai tsarin karba-karba a jam’iyyun siyasa.
Gwamna Wike
Gwamnan Ribas, Nyesom Wike Hoto: @GovWike
Asali: Facebook

Babu ta yadda shugaban jam’iyya na kasa da kuma ‘dan takarar shugaban kasa za su fito daga wuri daya.
Abin da muke cewa shi ne Ayu ya cika alkawari, ya yi murabus tun da ‘dan takaran shugaban kasa ya fito

Ka zo Ribas idan ka isa

Punch ta rahoto Gwamnan yana cewa idan har shugaban jam’iyyar yana ganin ya na da iko, ya zo jihar Ribas ya hana wani ‘dan takara shiga zabe mai zuwa.

“Ina kalubalantarsa ya zo jihar Ribas, ya hana wani ‘dan takara shiga zabe. Shin ku na so ku ci zabe? Shakka babu Jam’iyya tana cikin tsaka-mai-wuya.

Kara karanta wannan

Jigon PDP Ya Cigaba da Tallata Bola Tinubu Duk da Shi Yana Goyon bayan Atiku Abubakar

Na kalubalance shi, Ayu ya zo ya hana wani ‘dan takara shiga zabe. Ya san ba zai iya ba, bai da wannan ikon, ya zo Ribas, ina mai kalubalantar shi.

Ana neman murde zabe

Da aka yi hira da shi a gidan talabijin, kun ji labari Buba Galadima ya nemi Muhammadu Buhari yayi hattara domin ‘ya ‘yan APC na shirin magudi.

Injiniya Buba Galadima ya kara nanata rade-radin da ke yawo na cewa wasu na neman yadda za su yi domin a ki yin amfani da BVAS a zabukan 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel