Jam'iyyar PDP Ta Dare Gida Biyu a Katsina, Tsagi Daya Ya Dakatar da Dan Takarar Gwamna

Jam'iyyar PDP Ta Dare Gida Biyu a Katsina, Tsagi Daya Ya Dakatar da Dan Takarar Gwamna

  • Jam'iyyar PDP ta sake shiga sabon rikici a jihar Katsina, mutum biyu na ikirarin shugabancin jam'iyyar
  • Tsagin Alhaji Majigiri dake samun goyon baya daga Ibrahim Shema, sun sanar da dakatar da ɗan takarar gwamna Yakubu Lado
  • Da yake tsokaci kan batun, Lado Danmarke yace labarin jita-jita ce kawai matukar babu wata hujja a zahirance

Katsina - Babbar jam'iyyar adawa PDP a jihar Katsina ta sake shiga dambarwa biyo bayan wani yunkuri mai cike da ruɗani na tsige shugaban jam'iyya, Alhaji Yusuf Salisu Majigiri.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya ƙara tsananta yayin da ake zargin cewa an dakatar da ɗan takarar gwamna a zaɓen 2023, Yakubu Lado Ɗanmarke.

Tsagin ɗan takara, Lado Ɗanmarke, ya haɗa tawagar shugabannin PDP na wasu kananan hukumomi da masu ruwa da tsaki suka yanke cewa ba zai yuwu a bar kujerar shugaba hannun Majigiri ba, wanda ke neman takarar majalisar tarayya.

Kara karanta wannan

"Zamu Kawo Karshen Matsalar Tsaro Cikin Watanni Shida" Tinubu Ya Faɗi Matakan Da Zai Ɗauka

Tambarin jam'iyyar PDP.
Jam'iyyar PDP Ta Dare Gida Biyu a Katsina, Tsagi Daya Ya Dakatar da Dan Takarar Gwamna Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Bugu da ƙari, suna zargin cewa Majigiri, wanda ke samun goyon baya daga tsohon gwamna, Ibrahim Shehu Shema, na kokarin cin dunduniyar ɗan takarar gwamna ta bayan fage.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wata majiya a PDP tace sakamakon haka tsagin Lado suka taru suka tunbuke Majigiri daga kujerar shugaba kana suka zaɓi mataimakin shugaban jam'iyya na shiyyar Daura, Alhaji Lawal Danbaci, a matsayin muƙaddashin shugaba.

Wane mataki ɓangaren Majigiri suka ɗauka?

Da suke martani kan lamarin, Tsagin Majigiri sun ayyana Alhaji Lawal Uli a matsayin muƙaddashin shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Katsina.

Haka zalika sun kuma sanar da cewa jam'iyya ta dakatar da ɗan takararta na gwamna a zaɓe mai zuwa, Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke.

Babu wani abun damuwa zamu shawo kan komai - Majigiri

Yayin da aka nemi jin ta bakinsa, Majigiri ya ayyana rikicin a matsayin wanda ya saba faruwa inda ya jaddada cewa zasu shawo kan komai.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Wike Ya Tona Asirin Abinda Yasa Shugaban PDP Bai Son Yin Murabus

Yace:

"Da farko ni a ɓangare na batun tunbuke ni daga matsayin shugaban jam'iyya ba wani abun ɗaga jijiyar wuya bane saboda dama na riga na miƙa ragamar komai hannun mataimaki na kamar yadda doka ta tanada."
"Don haka wasu mutane su zauna su ce sun tsige ni ma bata taso ba, mai yuwuwa basu san bani ne a kujerar ba. Game da batun Lado, ina kallon lamarin kamar na kowane mutum, bani da hannu a ciki, ba zance komai ba."

Ban ɗauki lamarin dagaske ba - Lado

A ɓangarensa, ɗan takarar gwamnan Katsina a PDP, Lado Ɗanmarke, yace matukar babu wata hujja dake nuna goyon bayan ɗayan tsagin, batun jita-jita ce kawai da ba zai ce komai a kai ba.

"Kun taɓa ganin inda aka dakatar ɗan takarar gwamna haka nan kawai? Sun baku takarda ko suka fitar da sanarwa kan batun? duk jita-jita ce kawai idan baku da hujja."

Kara karanta wannan

2023: Yadda 'Yan Najeriya Zasu Ji Daɗi Sakamakon Ziyarar da Atiku Ya Kai Kasar Amurka

Duk wani yunkurin jin ta bakin shugaban PDP na riko, Lawal Uli, bai kai ga nasara ba domin bai ɗaga kiran waya ba kuma bai amsa sakonnin karta kwana da aka tura masa ba.

A wani labarin kuma Rikici Ya Tsananta, Jam'iyyar PDP Ta Kori Dan Takarar Gwamna da Wasu Mutum Uku

Rikicin PDP ya ƙara tsananta a jihar Ogun yayin da uwar jam'iyya ta ƙasa ta kori Jimi Lawal da wasu jiga-jigai kan wasu dalilai.

Wani kwamiti da NWC ta kafa na ladabtarwa karkashin jagorancin Barista Odulaja ne ya ba da wannan shawarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel