Dan a Mutum Peter Obi da Ya Hau Dutsen Kilimanjaro Don Kafa Tutar LP Ya Samu Lambar Yabo

Dan a Mutum Peter Obi da Ya Hau Dutsen Kilimanjaro Don Kafa Tutar LP Ya Samu Lambar Yabo

  • Gershon Ogbuluijah ya shafe awanni 10 da rabi domin hawa kan dutsen da ya fi kowanne tsawo a Afrika don kawai ya kafa tutar jam'iyyar Labour
  • Dutsen Kilimanjaro ne dutse mafi tsawo a Afrika da kuma a duniya idan ana maganar duste dake tsaye haikam shi kadai
  • Ogbuluijah ya yi karin haske kan dalilin da yasa ya dauki wannan mataki na zuwa har kasar Tanzania don kafa tutar su Peter Obi

Dan a mutun jam'iyyar LP da ya dale dutsen Kilimanjaro mafi tsawo a Afrika ya bayyana yadda ya shafe awanni 10 da rabi yana kokarin hawa don kafa tutar jam'iyyar su Peter Obi.

Gershon Ogbuluijah, mai shekaru 62 wanda dan asalin Ataba Kingdomi ne a karamar hukumar Andoni ta jihar Ribas ya yada bidiyonsa a daidai lokacin da ya kai kololuwar dusten.

Kara karanta wannan

Attajirin Mawakin da Ya yi Shekara 4 Bai Rike Kudi ba, Ya Rasa N850bn a Awa 24

Dan a mutun Peter Obi ya samu lambar yabo
Dan a mutum Peter Obi da ya hau Dutsen Kilimanjaro don kafa tutar LP ya samu lambar yabo | Hoto: OGersh
Asali: Twitter

Ya kuma yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa shi wai ba dan adam bane, wai shi mutun-mutumi ne.

Ya bayyana cewa, ya dawo Najeriya ranar Larabar da ta gabata 26 ga watan Oktoba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kau da jita-jita da karin bayani

Ga dai abin da ya rubuta a shafinsa na Twitter:

"Ina yin wannan karin bayanin ne saboda warware abubuwa kamar haka: 1. Ni ba mutun-mutumi bane. 2. Ni ba matashi bane amma ina jin takaicin da matasa ke ji, wannan yasa na yi hakan.
"3. A Najeriya nake rayuwa, na yi tafiya zuwa Tanzania a ranar 11 ga watan, na fara hawa dutse a ranar 15 ga wata na kuma kammala a ranar 20/10/222. 5. Na dawo Najerya awanni 6 da suka gabata."

A wani rubutu na daban da ya yada ya bayyana cewa, ya zabi fara hawan dusten ne a ranar Asabar domin samun daman kammala komai zuwa ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Bana Bukatar Matar Aure Tunda Na Iya Girki Da Goge-goge: Matashi Dan Shekaru 47 Ya Ki Aure

Ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta tun bayan sanun kabarin abin da ya aikata.

Mai Goyon Bayan Peter Obi Ya Hau Kololuwar Dutse Mafi Tsawo A Afirka Ya Kafa Tutar LP

A wani labarin, wani matashi mai goyon bayan jam'iyya Labour Party, LP, wadanda ke yi kansu lakabi da 'Obidients' ya nuna goyon bayansa ga jam'iyyar ta wani hanya mai ban mamaki.

Obidient din mai sna OGersh ya hau har kololuwar Dutsen Kilimanjaro a Tanzania, Dutse mafi tsawo a Afirka don sanar da duniya jam'iyyar ta LP.

Bayan shafe awanni 10 da rabi wurin hawa, tafiya da tattaki, OGersh ya isa kololuwar Dutsen inda ya kafa tutar Labour Party.

Asali: Legit.ng

Online view pixel