Bana Bukatar Matar Aure Tunda Na Iya Girki Da Goge-goge: Matashi Dan Shekaru 47 Ya Ki Aure

Bana Bukatar Matar Aure Tunda Na Iya Girki Da Goge-goge: Matashi Dan Shekaru 47 Ya Ki Aure

  • Wani dan Najeriya wanda ya gaji dukiyar mahaifinsa kuma shima yana da arziki ya ki yin aure duk da dangi sun nusar da shi kan yin hakan
  • A cewar wani danginsa, Timothy Obinna, mutumin ya ce tunda ya iya girki da tsaftar wuri, baya bukatar aure
  • Yan Najeriya da dama sun yi martani kan wannan hukunci nasa inda wasu suka yi sha'awar fadin gaskiya irin nasa

Wani dan Najeriya mai suna Timothy Obinna, ya haddasa cece-kuce kan furucin da yayi game da dalilin da yasa maza masu kudi basa son yin aure.

Wallafar Obinna martani ne ga wata wallafa da @Makavelli275 yayi inda yake mamakin dalilin da zai sa mutum da ke karbar albashi (N65,577,000) duk shekara zai dunga gudun aure.

Matashi na girki
Bana Bukatar Matar Aure Tunda Na Iya Girki Da Goge-goge: Matashi Dan Shekaru 47 Ya Ki Aure Hoto: iStockPhoto
Asali: UGC

Ya bayyana cewa yana da wani kawu da zai cika shekaru 48 a 2023 kuma ya ki yin aure.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa CBN Zata Sauya Wasu Takardun Kudaden Najeriya

Duk da cewar mutumin na cikin kudi kuma ya gaji arzikin mahaifinsa, ya bayyana cewa baya bukatar mace a rayuwarsa saboda shi ya iya girki da gyara sosai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake magana kan kawun nasa, Obinna ya kara da cewa:

“Amma ba zan yi karya ba gayen nan ya fi mahafiyata ma iya girki da gaske.”

Kalli wallafarsa a kasa:

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin mutane:

@veraidoko3 ya ce:

“Ina ganin zai iya samun yara da kansa don su gaji dukiyarsa saboda haka babu bukatar ya ajiye mata. Aikin banza.”

@LivingstoneB5 ya tambaya:

“Kana nufin…kana jin dadin abuncinsa/girkinsa fiye da mahaifiyarka?

Obinna ya yi martani:

“Dan uwa dangi sun shawarci sau da dama kan ya bude gidan abinci nasa na kansa, a iya sanina ban taba cin abincin da ya fi nasa dadi ba.”

Kara karanta wannan

Ta Rabu Da shi Saboda Tayi Sabon Saurayi: Magidanci Ya Ruguza Gidajen Da Ya Ginawa Matarsa Da Surukarsa

@Akinwole_Fenwa ya ce:

“Na san wani haka nima. Mutumin nan ya iya girki, gyare-gyare da kula da bakinsa. Duk sanda aka taso masa da maganar aure. Sai ya ce: “babu sauran matan kirki a waje dan Allah, bana sowa kaina wahala.”

Kyakkyawar Budurwa Mai Shekaru 38 Ta Bazama Neman Miji A Intanet,Ta Fashe Da Kuka A Bidiyo

A wani labarin, wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya mai suna Princess Mimi ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta koka kan cewa har yanzu bata auru ba duk da yawan shekarunta.

Matashiyar mai shekaru 38 ta wallafa wani bidiyo a TikTok inda ta dungi sharban kuka a cikin wata mota yayin da take fallasa asirin zuciyarta.

Princess ta ce zata cika shekaru 39 a bana, kuma har yanzu bata yi aure ko mallakar da nata na kanta ba kuma bata da wani tsayayye da zai fito neman aurenta.

Kara karanta wannan

A kirga lafiya: Bidiyon mutumin da yazo siyan kaya da jaka cike da 'yan N10 ya tada kura

Asali: Legit.ng

Online view pixel