Attajirin Mawakin da Ya yi Shekara 4 Bai Rike Kudi ba, Ya Rasa N850bn a Awa 24

Attajirin Mawakin da Ya yi Shekara 4 Bai Rike Kudi ba, Ya Rasa N850bn a Awa 24

  • Kanye West ya tabbatar da maganar da ake yi na cewa yanzu bai cikin wadanda suka mallaki akalla $1bn
  • Mawakin ya fadawa wani cewa shakka babu ya rasa Dala biliyan biyu daga cikin dukiyarsa a kwana daya
  • Amma Tauraron yace dama ba dukiya ne mutum ba, ana sanin asalin mutum ne wadanda ke tare da shi

America - Daya daga cikin manyan taurarin mawaka a Duniya, Kanye West ya tabbatar da rahoton da Forbes ta fitar a gaba da rasa dukiya da ya yi.

Jaridar The Nation ta gida ta rahoto Kanye West yana cewa ya yi asarar fam Dala biliyan 2 a rana daya. Hakan ya jawo ya fita daga sahun Biliniyoyi.

An zargi mawakin da nuna kiyayya ga yahudawa da bakaken fata, wannan ya jawo arzikinsa ya yi kasa, har ya sauka daga rukunin manyan Attajirai.

Kara karanta wannan

Bana Bukatar Matar Aure Tunda Na Iya Girki Da Goge-goge: Matashi Dan Shekaru 47 Ya Ki Aure

Tsohon mijin Kim Kardashian ya gamu da kalubale iri-iri sakamakon kalamansa. A makon nan kamfanin Adidas ya je yarjejeniyar da ya shiga da shi.

$1.5bn zuwa $400m

Tauraron da ake tunani ya mallaki fiye Dala biliyan 1.5 a asusun banki ya dawo yana da fam Dala miliyan 400 a sakamakon rasa manyan kwangiloli.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Forbes tace mawakin ya shaidawa wani 'dan kasuwa, Ari Emmanuel cewa duk da ya rasa Dala biliyan biyu a rana guda, yana nan da ransa, bai mutu ba.

Kanye West
Kanye West Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Kanye West wanda akan kira da Ye ya fitar da jawabi mara batanci domin ya wanke kan shi.

A jawabin da ya fitar, West mai shekara 45 ya tabbatarwa ‘ri Emmanuel cewa yana mai kaunarsa har gobe, haka zalika Ubangiji ma yana kaunarsa.

Mutane sune mutum - West

West wanda ya shahara da wake-wake da gayu yake cewa mutane sune kasuwa, ba rumfuna ba.

Kara karanta wannan

Yadda Wani Mutum Ya Makance Bayan Ya Auri Makauniya Da Mijinta Ya Tsere Ya Bar Ta, Sun Bada Labarin Soyayyarsu

“ARI EMMANUEL, NA RASA DALA BILIYAN BIYU A RANA DAYA KUMA GA NI DA RAI NA.
INA SON KA HAR YANZU. UBANGIJI YANA KAUNARKA. BA KUDI SUKA YI NI BA, MUTANE SUKA YI NI.

Shekara 4 bai taba kudi ba

Kwanakin baya an rahoto Kanye West yana cewa duk da irin dukiyar da ya mallaka, ya shafe kimanin shekaru hudu bai rike tsabar kudi da hannunsa ba.

Tauraron ya yi wannan bayani a wani bidiyo da wata mata ta dumfaro shi da kudi a hannunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel