Mai Goyon Bayan Peter Obi Ya Hau Kololuwar Dutse Mafi Tsawo A Afirka Ya Kafa Tutar LP

Mai Goyon Bayan Peter Obi Ya Hau Kololuwar Dutse Mafi Tsawo A Afirka Ya Kafa Tutar LP

  • Domin nuna goyon bayansa ga jam'iyyarsa ta Labour Party, wani matashi ya hau kololuwar Dutsen Kilimanjaro ya kafa tutar LP
  • OGersh, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter ya ce ya shafe awanni 10 da rabi yana hawa da tafiya kafin ya isa kololuwar dutsen
  • Ya ce babu wurin da ya fi dacewa a sanar da tahowar sabuwar Najeriya fiye da wuri mafi tsawo a Afirka, yana mai cewa wannan ne gudunmawarsa ga LP

Twitter - Wani matashi mai goyon bayan jam'iyya Labour Party, LP, wadanda ke yi kansu lakabi da 'Obidients' ya nuna goyon bayansa ga jam'iyyar ta wani hanya mai ban mamaki.

Obidient din mai sna OGersh ya hau har kololuwar Dutsen Kilimanjaro a Tanzania, Dutse mafi tsawo a Afirka don sanar da duniya jam'iyyar ta LP.

Kara karanta wannan

Musulmi da Kirista duk daya ne: Tinubu ya yiwa malaman addini jawabi a Kano

Dutsen Kilimanjaro
Mai Goyon Bayan Peter Obi Ya Hau Kololuwar Dutse Mafi Tsawo A Afirka Ya Kafa Tutar LP. Hoto: @OGersh.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayan shafe awanni 10 da rabi wurin hawa, tafiya da tattaki, OGersh ya isa kololuwar Dutsen inda ya kafa tutar Labour Party.

A cewar shafinsa na Twitter, dutsen da ya fi kowanne tsawo a Afirka shine wurin da ya fi dacewa don sanar da abin da Najeriya ke daf da haifar wa.

OGersh yayin wallafa hotonsa yana nuna tutan LP a koluluwar Dutsen ya ce:

"A ranar Juma'a, 20/10/2022 bayan shafe awa 10 1/2 na hawa, tattaki da tafiya, Na isa kololuwar dutsen na Kilimanjaro, mai nisan 5,895 sama da matakin teku.
"Babu wurin da ya fi dacewa a sanar da zuwan sabuwar Najeriya fiye da jinkar Afirka."

Zaben 2023: Peter Obi Ya Ce Ko Ƴaƴan Cikinsa Ba Su Yarda Da Shi Idan Ya Yi Alƙawari, Mutane Sun Yi Martani

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Allah Ya Yiwa Dan Tsohon Ministan Buhari Rasuwa

A wani labarin, Mr Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, LP, yana shan suka a soshiyal midiya saboda amsar da ya bada kan tambayar da aka masa game da yadda zai farfado da lantarki a Najeriya.

Mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin na Arise TV ya ce wannan shine dalilin da yasa ya kamata dan takarar LP din ya fitar da manufofinsa ga kasar a rubuce don mutane su gani su yi nazari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel