Tinubu da Na Son Kai, Ba Zan Zabe Shi Ba a Zaben 2023, in Ji Farfesa Akintoye

Tinubu da Na Son Kai, Ba Zan Zabe Shi Ba a Zaben 2023, in Ji Farfesa Akintoye

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu na ci gaba da samun kiyayya daga kabilarsa
  • Kamar dai yadda kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta nuna adawa da tafiyar Tinubu, haka nan wata kungiya ta Yarbawa ta nuna kin jinin takararsa
  • Shugaban kungiyar, Farfesa Banji Akintoye ya siffanta kadan daga halayen Tinubu, don haka yace ba zai zabe shi ba

Najeriya - Gabanin zaben 2023 na shugaban kasa, farfesa Banji Akintoye, shugaban kungiyar Yarbawa ta Yoruba Nation Self-Determination Struggle ya bayyana kadan daga halin dan takarar shugaban kasa na APC.

Ya kuma bayyana cewa, tabbas ba zai zabi Bola Ahmad Tinubu ba saboda wasu dalilai da ya bayyana.

Ba zan zabi Tinubu ba, yana da son kai, inji shugaban Yarbawa
Tinubu da na son kai, ba zan zabe shi ba a zaben 2023, in ji Farfesa Akintoye | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwar da jaridar Punch ta wallafa a ranar Alhamis 27 ga watan Oktoba, farfesa Akintoye ya ce Tinubu na son zama shugaban kasa ne kawai don cimma wata manufa ta kashin kai.

Kara karanta wannan

2023: Ɗaliban Najeriya Sun Goyi Bayan Takarar Tinubu Da Shettima, Sun Bada Ƙwakwarar Dalili

Da yake tuna batun Tinubu a jihar Ogun na cewa 2023 layinsa ne ya zama shugaban kasa, Akintoye ya ce maganganun Tinubu sun nuna shi a matsayin mutum mai son kansa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

"Dan uwanmu, Tinubu, kana fafutuka ne wa karan kanta kadai yayin da danginka gaba daya ke cikin halaka.
"Akwai wuta a kanmu a matsayinmu na kasa. Wa zai yarda ace akwai Bayarben dake yiwa al'ummarsa abin da ka kake yiwa mutanenka."

Tinubu ya fito takara a lokacin da bai dace ba, inji Akintoye

Farfesan na fannin tarihi ya bayyana cewa, Tinubu ya fito takara a 2023, amma ya fito a lokacin da bai dace ba, rahoton Vannguard.

Sai dai, an ruwaito cewa, akwai lokacin da farfesan ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu, duk da cewa ya yi bayani a yanzu kan matsayarsa game da dan takarar na APC.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Ta karewa Atiku, gwamnan Arewa na PDP da dattawan jiharsa sun ce ba sa yinsa

A sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis, 27 ga watan Oktoba, ya bayyana cewa, a yanzu dai bai da niyyar zaben Tinubu a zaben 2023 mai zuwa.

Manyan Yan Kasuwan Arewa, Kungiyar Malamai Kano, Manyan Tijjaniyya da Kadiriyya Sun Bayyana Goyon Bayan Tinubu

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya sake samun karbuwa a idon manyan jiga-jigan yankin Arewacin Najeriya, musamman Kano.

Jiga-jigan masu fada a ji a Arewacin Najeriya da suka hada da 'yan kasuwa da malamai sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC.

A jihar Kano, shugabannin 'yan kasuwa, malamai, 'yan Tijjaniya, Ahlus Sunnah da 'yan Kadiriyyah ne suka bayyana goyon bayansu gareshi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel