Gwamna Wike da Wasu Gwamnoni Hudu Sun Sake Kauracewa Gamgamin Atiku a Edo

Gwamna Wike da Wasu Gwamnoni Hudu Sun Sake Kauracewa Gamgamin Atiku a Edo

  • Gangamin taron yakin neman zaɓen shugaban kasa na PDP da ya gudana a jihar Edo ya kara fito da rikicin jam'iyyar
  • Wasu gwamnoni dake kan madafun iko 5 sun kaurace wa taron, wasu kuma sun halarta ranar Asabar
  • Gwamna Wike da yan tawagarsa na ci gaba da kiran shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, ya yi murabus

Gwamnoni Biyar dake takun saƙa da bangaren shugabancin jam'iyyar PDP na ƙasa ba su halarci gangamin taron yakin neman zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana a jihar Edo ba ranar Asabar.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa gangamin Kamfen wanda ya gudana a Benin, babban birnin jihar Edo, ya samu halartar wasu gwamnonin PDP, mambobin kwamitin gudanarwa (NWC) da na BoT.

Gwamna Wike da yan tawagarsa.
Gwamna Wike da Wasu Gwamnoni Hudu Sun Sake Kauracewa Gamgamin Atiku a Edo Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Atiku Abubakar, mai neman zama shugaban kasa a inuwar PDP ya diro Najeriya ranar Jumu'a kafin zuwan ranar taron.

Kara karanta wannan

Na Kusa da Gwamnan Arewa, Mataimakin Shugaban PDP da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma APC

Gwamnonin PDP da suka je wurin

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo watau mai tarban baƙi, da gwamna Emmanuel Udom na jihar Akwa Ibom sun halarci gangamin kamfen PDP a Edo.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka zalika waɗan da aka hanga sun mamaye filin tallata Atiku daga cikin gwamnonin har da Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato, Darakta Janar na kwamitin kamfe da Ifeanyi Okowa na jihar Delta, abokin takarar Atiku.

Jerin gwamnonin da suka kaurace wa taron

Sai dai kuma gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da sauran gwanonin PDP dake mara masa baya sun tsallake gangamin kamfen, ba'a hange su a wurin ba

Gwamnonin dake tare da Wike sun haɗa da gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, Seyi Makinde na jihar Oyo, Okezie Ikpeazu na jihar Abiya da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa gwamnonin guda biyar ba su halarci ko ɗaya daga cikin tarukan kamfen PDP ba tun bayan buɗe wa a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Ana Zargin Abba Ganduje Da Laifin Karkatar Da Dukiyar Gwamnati, An Kai Kararsa Wajen EFCC

Gwamna Wike da ake kallon shi ne jagoransu, ba da jimawan nan ba ya sake jaddada bukatar dole shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, ya yi murabus.

Bukatar Ayu ya sauka daga kujerarsa ta ƙara karfi ne kan hujjar cewa bai kamata shugaban jam'iyya da ɗan taƙarar shugaban ƙasa sun fito daga yanki ɗaya ba.

Sai dai wasu ƙusoshin jam'iyyar PDP sun yi fatali da bukatar, inda suka ce zai sauka ne kaɗai bayan Atiku ya lashe zaben shugaban ƙasa a 2023.

A wani labarin kuma kun ji cewa Gwamna Wike Ya Kara Kaɗa Hanjin PDP Kan Wanda Ya Dace Ya Gaji Buhari a 2023

Gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ya shawarci yan Najeriya su zabi ɗan takarar shugaban ƙasa wanda ke da kwarewar shugabanci.

Wike, wanda ya yi jawabi a wurin wani taro a Legas, yace ya kamata yan Najeriya su guji mutanen dake magana kan kabilanci.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Jam'iyyar APC Ta Fitar da Sunayen Tawagar Kamfen 2023 Na Karshe, An Samu Sauyi

Asali: Legit.ng

Online view pixel