PDP a Jihar Arewa Ta Yi Wa Atiku Abubakar Alkawarin Kuri'u Miliyan Biyu a Zaben 2023

PDP a Jihar Arewa Ta Yi Wa Atiku Abubakar Alkawarin Kuri'u Miliyan Biyu a Zaben 2023

  • Jam'iyyar PDP reshen jihar Plateau ta dauki alkawarin kawowa Atiku Abubakar kuri'u miliyan biyu gabannin 2023
  • Babbar jam'iyyar adawar kasar ta kuma sha alwashin lashe dukkanin kujerun siyasa a jihar
  • Shugabannin jam'iyyar sun bayyana hakan ne a yayin kaddamar da kungiyar kamfen din Atiku-Mutfwang a Jos

Plateau - Jam’iyyar PDP a Plateau ta yi alkawarin kawowa dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, kuri’u miliyan biyu a 2023 da kuma lashe duk wasu mukaman siyasa a jihar.

Jiga-jigan jam’iyyar a jihar sun bayyana hakan ne a yayin bikin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben Atiku-Mutfwang a Jos, babban birnin jihar, rahoton AIT.

Atiku Abubakar
PDP a Jihar Arewa Ta Yi Wa Atiku Abubakar Alkawarin Kuri'u Miliyan Biyu a Zaben 2023 Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: UGC

Dandazon magoya bayan jam'iyyar sun halarci bikin kaddamar da kwamitin kamfen din na Atiku-Mutfwang gabbanin zaben 2023.

Dan takarar gwamnan PDP, Caleb Mutfwang, wanda ya kaddamar da kwamitin kamfen din ya ce zai jagoranci kawowa Atiku da duk yan takarar PDP a Plateau kuri’un jama’ar jihar.

Kara karanta wannan

Atiku Na Kara Samun Karfi Yayin da Mambobin APC 1,000 Suka Sauya Sheka Zuwa PDP a Wata Jahar Kudu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabinsa, shugaban PDP a jihar, Chris Hassan ya ce bikin kaddamar da kwamitin shine masomin kwato gwamnatin Plateau da Najeriya yayin da yake ba da tabbacin cewa Atiku zai samu fiye da kuri’u miliyan biyu a jihar.

A nasu jawain, tsohon jakadan Najeriya a Switzerland, Yahaya Kwande da sauran shugabannin jam’iyyar sun nuna karfin gwiwar cewa jam’iyyar za ta yi nasara a babban zaben mai zuwa.

Idan Atiku Ya Lashe Zaben 2023 Yan Kudu Sun Shiga Uku, Sagay

A wani labarin, shugaban kwamitin PACAC, Farfesa Itse Sagay ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya fallasa kansa a matsayin wanda ke kyamar yan kudu.

Sagay wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin, 17 ga watan Oktoba, ya bayyana cewa mutanen kudu zasu dandana kudarsu idan har Atiku ya kashe babban zaben 2023 mai zuwa, rahoton Daily Independent.

Kara karanta wannan

Jerin Gwamnonin PDP da Suka Gindaya Sharuda Kafin Su Goyi Bayan Atiku Abubakar

Atiku, a wajen wani taron da kwamitin hadin gwiwa na arewa ya shirya, ya bukaci mutanen arewa da kada su zabi dan takarar shugaban kasa Bayarabe ko Ibo a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel