Tsohon ‘Dan Majalisa Ya Sanar da Barin APC Ranar da Tinubu ya Kaddamar da Manufofi

Tsohon ‘Dan Majalisa Ya Sanar da Barin APC Ranar da Tinubu ya Kaddamar da Manufofi

  • Jam’iyyar APC ta rasa wani daga cikin ‘ya ‘yanta a jihar Neja, a sakamakon sauya-sheka na 'yan siyasa
  • Hon. Ibrahim Ebbo ya bada sanarwar ficewa daga APC mai mulki a lokacin da ake soma kamfe na 2023
  • A wasikar da ya aika, tsohon ‘dan majalisar tarayyar yace ya canza sheka ne saboda ganin damarsa

Niger – Sauya-shekar da ake yi ya taba jam’iyyar APC mai mulkin jihar Neja, inda aka ji Hon. Ibrahim Ebbo ya bada sanarwar barin jam’iyyar.

Kamar yadda muka samu labari daga shafin sada zumunta na Facebook, tsohon ‘dan majalisar tarayya ya rubuta takarda cewa ya fice daga APC.

Ibrahim Ebbo ya aika wasika zuwa ga shugaban jam’iyyar APC na mazabar Ebbo/Gbacinku da ke karamar hukumar Lapai, yana mai sanar da hakan.

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

Legit.ng tace ‘Dan siyasar wanda ya taba wakiltar mutanen mazabar Lapai/Agaie a majalisar wakilai a shekarun baya bai bayyana inda da zai koma ba.

A wasikar da ya rubuta a ranar 19 ga watan Oktoba, Hon. Ebbo yake cewa ganin damansa ne kurum ta sa ya bar jam’iyya mai mulki watau APC.

Wasikar Ibrahim Ebbo

“Ina mai rubuto maka wannan domin sanar da kai cewa na yi murabus daga zama ‘dan jam’iyyar Progressives Congress (APC), ba tare da wata-wata ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tsohon ‘Dan Majalisa
Hon. Ibrahim Ebbo ya bar APC Hoto: Hon Ibrahim Abdul Ebbo
Asali: Facebook

Shakka babu na shiga tsaka mai-wuya a irin wannan lokaci, amma abin da ya fi dacewa da ni kenan.”
“Akwai bukatar in nuna godiya ta mara iyaka ga shugabannn jam’iyya na matakin mazaba har zuwa tarayya, da nayi aiki a kwamitin shugabanni.”

Wace jam'iyya ya koma?

Independent tace wani tsohon Kwamishina a gwamnatin Abdulkadir Kure kuma Mai ba Gwamna Abubakar Sani Bello ya tabbatar da wannan labari.

Kara karanta wannan

Tsohon Na Hannun Daman Kwankwaso Ya ki Yarda Ya yi Aiki a Kwamitin Kamfen Peter Obi

Olayinka Lere mai neman takarar ‘dan majalisar tarayya na mazabar Ekiti ta tsakiya a 2023, ya yi ikirari a Facebook cewa Ebbo ya shigo jam’iyyar PDP.

Lere yana cikin hadiman Ayodele Fayose a lokacin yana gwamna a Ekiti tsakanin 2014 da 2018.

Fasto ba zai yi wa APC aiki ba

An samu labari cewa Gideon Para-Mallam yace ba zai yi aiki da kwamitin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC da aka ga sunan shi ya fito ba.

A jawabin da ya fitar Rabaren Gideon Para-Mallam yace ba a tuntube shi kafin a sa sunansa, kuma yana tare da CAN mai adawa da tikitin musulmai biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel