Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

  • An samu wasu daga cikin ‘Yan majalisar NWC PDP da ke kukan ba a damawa da su a yakin zaben 2023
  • Stella Effah-Attoe wanda ke rike da kujerar Shugabar mata ta kasa a PDP tace an maida ta saniyar ware
  • Wasu suna zargin Iyorchia Ayu ba ya tafiya da ‘Yan siyasar Kudancin Najeriya a shirin takarar Atiku

Abuja - Rikicin cikin gidan da ya bijirowa jam’iyyar adawa ta PDP bai da niyyar karewa, sai dai ma aka ji ya dauki wani salo na dabam kwanan nan.

A wani rahoto da ya fito daga Punch, an ji cewa wasu daga cikin ‘yan majalisar NWC suna zargin Iyorchia Ayu da maida su saniyar ware a wajen kamfe.

Shugabar mata ta kasa a jam’iyyar PDP, Stella Effah-Attoe ta fitar da jawabi tana cewa ana yunkurin yin watsi da ita a yakin neman zaben shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Shugabar Hukumar NIDCOM Ta Cire Rigar Mutunci, Ta Dirkawa Wani Zagi a Twitter

Duk da muhimmiyar kujerar da take rike da ita, Stella Effah-Attoe ta rubuta takardar korafi, tana bayanin yadda ake wulakanta ta wajen taron kamfe na PDP.

Korafin Farfesa Stella Effah-Attoe

A cewar shugabar matan jam’iyyar hamayyar, kiri-kiri aka hana ta yi wa jama’a bayani a gangamin da aka yi a Uyo, duk da a al’ada ba haka abin yake ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Effah-Attoe tace a jihar Akwa Ibom, Sanata Uche Ekwunife aka sa tayi wa mata jawabi. Da aka je yi wa Atiku kamfe a Kaduna, sai aka kira Baraka Sani.

Yakin Zaben Atiku
Atiku Abubakar a Kaduna Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Shugabar matar tace a ka’ida idan an je wani taron siyasa, ana kiran shugabar mata da shugaban matasa na kasa suyi wa ‘yanuwansu mata da matasa jawabi.

Dole a tafi da mutanen Kudu

Bode George wanda ya taba rike mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, ya zargi Iyorchia Ayu da ‘yan majalisarsa da neman watsi da mutanen Kudu.

Kara karanta wannan

2023: Kura Ta Kara Turnuke Wa Atiku, Shugabannin PDP a Wata Jiha Sun Yi Fatali da Sunayen Tawagar Kamfe

An rahoto Cif George yana jan-kunnen jam’iyyar hamayyar cewa ka da a maida ‘yan Kudu tamkar 'yan bora a PDP, a hada-kai domin ayi nasara a zaben 2023.

Hakan na zuwa ne a lokacin Stella Effah-Attoe da wasu ‘yan majalisar NWC suka dawo da kudin da aka aika masu, suna kalubalantar aikin Iyorchia Ayu.

Taofeek Arapaja, Dan Orbih, Alli Adagunobi-Oluwatukesi, da kuma Setonji Koshoedo sun maidowa jam’iyya da miliyoyin da aka biya su da sunan kudin otel.

Shugaban PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu ya maidawa abokan aikinsa martani da cewa sun san da batun kudin, kuma ba a saba doka a dalilin hakan ba.

APC tayi wasu gyare-gyare

A ranar Laraba aka ji labari jam'iyyar APC ta fitar da jerin sunayen 'ya 'yan kwamitin yaƙin neman zaben Tinubu/Shettima 2023, an samu sauye-sauye a jerin.

Gwamnoni da manyan masu ruwa da tsaki a APC sun nuna rashin amincewa da tawagar farko da aka fitar, lamarin da ya haddasa tsaiko a shirin Kamfe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel