Kwamitin Takara: Fasto ya Kunyata APC, Yace Ba Zai Yi Wa Tinubu Kamfe a 2023 ba

Kwamitin Takara: Fasto ya Kunyata APC, Yace Ba Zai Yi Wa Tinubu Kamfe a 2023 ba

  • Gideon Para-Mallam ba zai yi aiki da kwamitin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki ba
  • A jawabin da ya fitar a ranar Juma’a, Rabaren Gideon Para-Mallam yace ba a tuntube shi kafin a sa sunansa ba
  • Faston yana tare da kungiyar CAN wanda ba ta goyon bayan tikitin Musulmi da Musulmi da jam’iyyar APC tayi

Jos - Rabaren Gideon Para-Mallam ya ki amincewa ya yi wa jam’iyyar APC aiki bayan an sa shi a ‘yan kwamitin neman zaben shugaban Najeriya.

Rabaren Gideon Para-Mallam ya yi watsi da wannan aiki ne lura da matsayin da kungiyar CAN ta dauko, Vanguard ta fitar da wannan rahoto a dazu.

Malamin addinin yace babu abin da ya hada shi da siyasar jam’iyya, amma yana tare da kungiyar kiristocin Najeriya da ke adawa da tikitin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Yadda Aka Yi Rabon Biredi A Wajen Wani Kasaitaccen Biki Na Gani Na Fada, Bidiyon Ya Ja Hankali

A wani jawabi da ya fitar a babban birnin Filato watau Jos, Faston yace shi ko matarsa da aka sa sunansu a kwamitin kamfe, ba su san da batun ba.

An rahoto Faston yana cewa jam’iyyar APC ba ta tuntube su kafin cusa sunayensu a kwamitin ba.

Bola Tinubu
Bola Tinubu a Ekiti Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabin Gideon Para-Mallam

"An jawo hankalina ga wani jerin sunaye da ke yawo da ya nuna ni (ko mai daki na – Farfesa Para-Mallam) ya shiga kwamitin neman zaben shugaban kasa na APC.
Babu wani daga cikinmu da ya san da wannan lamarin, kuma ba a nemi izinin ba.
Ni ba ‘dan siyasa ba ne, malamin addini ne ni, kuma mai rajin ganin an kawo zaman lafiya. Ba na siyasa. Kuma ni ba ‘dan wata jam’iyyar siyasa a Najeriya ba ne.

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

Baya ga haka, CAN ta dauki matsaya, tana adawa da tikitin Musulmi-Musulmi ko na wani Kirista-Kirista."

Ina tare da CAN - Gideon Para-Mallam

"Ina mai girmama wannan mataki da aka dauka. Najeriya kasa ce mai kabilu, al’adu da addinai da-dama. Ya kamata a nuna wannan a yadda jam’iyyunmu ke aiki.
Yarda in yi aiki a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasan APC yana nufin nayi watsi da wannan ginshiki na cewa mu kasa ce mai mabanbantan addini."

- Gideon Para-Mallam

A karshe, Faston ya nesanta kan shi da abin da ya shafi kamfe a 2023, yace yana da abokai a duka jam’iyyu, amma zai cigaba da kokarin kawo zaman lafiya.

Manufofin Bola Tinubu

A yau ne aka ji alkawuran da ke kunshe a cikin takardar manufofin ‘Dan takaran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu sun hada da samar da tsaro.

Bola Tinubu ya yi alkawarin cigaba da bunkasa harkar noma, tare da kawo manufofin da za su inganta tattalin arziki da rage talauci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Jam'iyyar APC Ta Fitar da Sunayen Tawagar Kamfen 2023 Na Karshe, An Samu Sauyi

Asali: Legit.ng

Online view pixel