INEC Ta Damu Matuka da Rikicin da Ake Samu a Wuraren Yakin Neman Zabe, Ta Gargadi Jam’iyyu

INEC Ta Damu Matuka da Rikicin da Ake Samu a Wuraren Yakin Neman Zabe, Ta Gargadi Jam’iyyu

  • Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta bayyana kadan daga tsoron da take ciki tun bayan fara gangamin kamfen a Najeriya
  • Jam'iyyun siyasa na ci gaba da rikici da juna, lamarin da ka iya kaiwa ga zubar da jini idan ba a samar da mafita ba
  • Lokatan kamfen a Najeriya na zuwa da sauyin yanayi, inda magoya bayan jam'iyyu ke ruwa da tsaki don tallata 'yan takararsu a sassan kasar

FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana kaduwa da damuwa game da abubuwan dake faruwa na rikici tsakanin jami'iyyun siyasa a fadin kasar nan.

Hukumar ya damuwa da yadda magoya bayan jam'iyyun siyasa ke yin kare jini biri jini a lokutan da suke yawon gangami a Najeriya, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Ku Zabi Tinubu Zai Kare Muradun Arewacin Najeriya, Sanata Abu Ibrahim

INEC ta fusata, ya fara yiwa jam'iyyun siyasa gargadi
INEC Ta Damu Matuka da Rikicin da Ake Samu a Wuraren Yakin Neman Zabe, Ta Gargadi Jam’iyyu | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shugaban INEC, Mahmood Yakubu ya bayyana kokensa ne a ranar Talata 18 ga watan Oktoba a wani taron horarwa na fasaha da hukumar ta gudanar kan zaben 2023.

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Musabbabin rikici tsakanin jam'iyyun siyasa da magoya bayansu a wasu jihohin kasar nan a lokutan gangamin kamfen babban abin damuwa ne.
“Haka nan, akwai barazanar hana jam’iyyu da ’yan takara shiga wasu wurare mallakin gwamnati a wasu jihohin tarayyar kasar nan.
"Ina gargadin jam'iyyun siyasa da magoya bayansu da su mai da hankali ga lamuransu kuma su guje takalar juna."

A bangare guda, ya ce hukumar za ta ci gaba sa ido don tabbatar da an gudanar kamfen cikin kwanciyar hankali, har da zabukan da za a gudanar a shekara mai zuwa, inji rahoton BusinessDay.

Gwamna El-Rufai Ya Tuna da Irin Rashin Mutuncin da Peter Obi Ya Yi Masa a 2013

Kara karanta wannan

Jigon PDP: Mun daina aikata zunubi saboda Atiku ya lashe zaben 2023

A wani labarin, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya bayyana a wani faifan bidiyon da TVC ta yada, inda yake bayyana kadan daga abu mara dadi da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi ya yi masa.

Ya tuna cewa, a shekarar 2013, ya kai ziyarar duba zabe a jihar Anambra, a nan ne dai Obi ya tsare shi tare da kokarin tozarta shi saboda a lokacin baya rike da mukamin gwamna.

A cewarsa, yanzu kuma shine gwamna a jihar Kaduna, gashi kuma Peter Obi, wanda a yanzu dan takarar shugaban kasa ne a jam'iyyar Labour zai shigo jiharsa, amma ba zai masa komai ba saboda shi wayayye ne kuma mai sanin ya kamata, cikakken dan Arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel