Gwamna El-Rufai Ya Tuna da Irin Rashin Mutuncin da Peter Obi Ya Yi Masa a 2013

Gwamna El-Rufai Ya Tuna da Irin Rashin Mutuncin da Peter Obi Ya Yi Masa a 2013

  • Gwamnan jihar Kaduna ya tono kadan daga cin zarafin da tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi ya yi masa
  • Ya bayyana yadda aka tozarta shi yayin da ya kai ziyarar duba aikin zaben gwamnan da aka yi a jihar Anambra a 2013
  • A makon nan ne Peter Obi ya daura aniyar yin gangamin kamfen dinsa a jihar Kaduna, jihar da El-Rufai ke mulka a yanzu

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya bayyana a wani faifan bidiyon da TVC ta yada, inda yake bayyana kadan daga abu mara dadi da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi ya yi masa.

Ya tuna cewa, a shekarar 2013, ya kai ziyarar duba zabe a jihar Anambra, a nan ne dai Obi ya tsare shi tare da kokarin tozarta shi saboda a lokacin baya rike da mukamin gwamna.

Kara karanta wannan

Jigon PDP: Mun daina aikata zunubi saboda Atiku ya lashe zaben 2023

Malam Nasiru El-Rufai ya tuna irin cin zarafin da Peter Obi ya yi masa a 2013
Gwamna El-Rufai Ya Tuna da Irin Rashin Mutuncin da Peter Obi Ya Yi Masa a 2013 | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cewarsa, yanzu kuma shine gwamna a jihar Kaduna, gashi kuma Peter Obi, wanda a yanzu dan takarar shugaban kasa ne a jam'iyyar Labour zai shigo jiharsa, amma ba zai masa komai ba saboda shi wayayye ne kuma mai sanin ya kamata, cikakken dan Arewa.

Ya kuma shaida cewa, 'yan Arewa na da karamci, kuma ba sa irin wannan aika-aika da Peter Obi ya yi masa a shekarar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanin El-Rufai mai ban mamaki

A kalaman Mallam:

"A 2013, na je jihar Anambra a matsayina na jigon APC domin shaida zaben da aka gudanar na gwamna, bakonku na gaba, Peter Obi lokacin yana gwamna, ya sa aka kama ni, aka tsare ni na tsawon awanni 48 a daki na na otal.
"A yau nine gwamnan jihar Kaduna, kuma zai zo jihar Kaduna. Kari kan 'yan sanda SSS da nake dasu, ina da wadatattun sojojin Najeriya masu makamai anan idan ina son kamawa da tsare kowa. Amma mu 'yan Arewa ne. Mu wayayyu ne. Ba ma aikata irin wannan."

Kara karanta wannan

Buhari: Na yi ayyuka masu tasirin da 'yan Najeriya ke alfahari dasu a fadin kasar nan

Kalli bidiyon:

Mun Daina Zunubi Domin Dan Takaranmu Atiku Ya Samu Nasara, Inji Dino Melaye

A wani labarin, mai magana da yawun kwamitin kamfen din jam'iyyar PDP a gangamin zaben shugaban kasa na 2023, Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa, wasu mambobin majalisar sun daina aikata zunubi saboda nemawa Tiku nasara a zabe mai zuwa.

Melaye ya bayyana hakan ne a wani taro da mambobin jam'iyyar PDP a jihar Kaduna, inda gangamin kamfen din jam'iyyar ya gudana, Daily Trust ta ruwaito.

Ya karanto wasu ayoyin Al-Qur'ani tare da cewa, wasu jiga-jigan PDP sun kame daga aikata zunubu ne domin kwadayin Allah ya amsa addu'arsu idan suka roke shi game da nasarar Atiku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel