Mun Daina Zunubi Domin Dan Takaranmu Atiku Ya Samu Nasara, Inji Dino Melaye

Mun Daina Zunubi Domin Dan Takaranmu Atiku Ya Samu Nasara, Inji Dino Melaye

  • Tsohon sanata kuma jigon jam'iyyar PDP ya bayyana cewa, yanzu dai ya daina aikata zunubu saboda Atiku ya ci zabe
  • Ya bayyana hakan ne taron gangamin kamfen din da ake a shirin zaben 2023 mai zuwa a nan da badi
  • Ana ci gaba da shirin zaben 2023, inda za a gwabza tsakanin 'yan takara daban-daban daga jam'iyyun kasar

Kaduna - Mai magana da yawun kwamitin kamfen din jam'iyyar PDP a gangamin zaben shugaban kasa na 2023, Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa, wasu mambobin majalisar sun daina aikata zunubi saboda nemawa Tiku nasara a zabe mai zuwa.

Melaye ya bayyana hakan ne a wani taro da mambobin jam'iyyar PDP a jihar Kaduna, inda gangamin kamfen din jam'iyyar ya gudana, Daily Trust ta ruwaito.

Ya karanto wasu ayoyin Al-Qur'ani tare da cewa, wasu jiga-jigan PDP sun kame daga aikata zunubu ne domin kwadayin Allah ya amsa addu'arsu idan suka roke shi game da nasarar Atiku.

PDP ta kama jihar Kaduna, za ta yi abin kirki a jihar a zabe mai zuwa

A bangare guda, Melaye ya caccaki jam'iyyar APC mai mukli, inda ya yace jam'iyyar bata isa kawo gangamin kamfen dinta jihar Kaduna ba.

Ya kuma bayyana cewa, jam'iyyar PDP a yanzu na da jiga-jigai daga tsoffin gwamnonin jihar, ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika, ya ce a yanzu jam'iyyar na da tsohon gwamna Makarfi da Ramalan Yero, duk a tafiyar da ake ta Atiku a zaben 2023 mai zuwa.

Ya kuma bayyana cewa, idan ana maganar zabe a yanzu, to tabbas PDP ta kama jihar Kaduna, kuma za ta haifar da da mai ido.

A wani rahoton na daban daga jaridar Vanguard, Dino Melaye ya ce 'yan Najeriya su guje APC, su zabi PDP a zabe mai zuwa.

Tinubu Ya Gaji, Kamata Yayi Ya Koma Gida Ya Yi Hutawarsa, Inji Na Hannun Daman Atiku

A wani labarin, jigon jam'iyyar PDP Phrank Shaibu ya caccaki dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.

A wata sanarwa da ya aikewa Legit.ng a jiya Lahadi 16 ga watan Oktoba, Shaibu ya bayyana cewa, duba da lafiyar Tinubu, bai cancanci ya gaji shugaban kasa Buhari ba.

Ya kuma bayyana cewa, Tinubu ya sha kwabsawa a maganganunsa tun bayan da ayyana aniyarsa ta zama shugaban kasa, wanda hakan ke nuna a rude yake gaba daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel