Tinubu Zai Kare Muradun Arewacin Najeriya, Sanata Abu Ibrahim

Tinubu Zai Kare Muradun Arewacin Najeriya, Sanata Abu Ibrahim

  • Abu Ibrahim, ya bayyana cewa dan takaran kujeran shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, zai kare muradun Arewa
  • Ya yi kira da yan Arewacin Najeriya su tuna Tinubu ya taimakawa dan Arewa (Buhari) a baya
  • Asiwaju Bola Tinubu ya tafi jihar Kaduna ranar Litnin don tattaunawa da dattawan Arewa

Tsohon Sanata da ya wakilci Katsina Ta Kudu a majalisar dattawa, Abu Ibrahim, ya bayyana cewa dan takaran kujeran shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, zai kare muradun Arewa.

Ibrahim ya bayyana hakan ranar Alhamis yayinda ya ziyarci ofishin kamfen Dikko Radda dan takarar gwamnan jihar na APC.

Sanatan yace lokaci ya yi da ya kamata Arewa ta mayarwa Tinubu alherin da ya yiwa yan yankin ta hanyar kada masa kuri'a, rahoton NAN.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Tinubu Ya Nemi Atiku Ya Janye Daga Takara, Ya Goya Masa Baya a 2023

Ya bayyana cewa Tinubu ya taka rawar gani wajen nasarar zaman Buhari shugaban kasa a 2015 da 2019.

Yace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Idan aka zabesa, Tinubu tabbas zai kare muradun Arewa."
Abu Ibrahim
Tinubu Zai Kare Muradun Arewacin Najeriya, Sanata Abu Ibrahim Hoton
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel