Kungiyar Inyamurai Ta Ohanaeze Ta Bukaci Atiku Ya Nemi Afuwa Kan Kalamansa da Ka Iya Raba Kai

Kungiyar Inyamurai Ta Ohanaeze Ta Bukaci Atiku Ya Nemi Afuwa Kan Kalamansa da Ka Iya Raba Kai

  • Kungiyar Inyamurai ta Ohanaeze ta bayyana bacin ranta da kalaman Atiku na cewa, 'yan Arewa su zabe shi su mance wasu kabilu
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da jam'iyyun siyasa a Najeriya ke ci gaba da tallata 'yan takara gabanin zaben 2023
  • Atiku ya ce, 'yan Arewa su zabe shi, kada su zabi Inyamuri ko Bayarbe saboda shi ya fi cancanta ya samu kuri'unsu

Najeriya - Kungiyar kabilar Inyamurai ta Ohanaeze ta yi kira ga dan takarar shugaban kasan jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da ya nemi afuwar Inyamurai da sauran al'ummar Kuduncin kasar nan kan maganar da ya yi a kwanan nan.

Kungiyar ta zargi Atiku da yin kalamai masu iya raba kan siyasar kasar nan a lokacin wani taron gangamin kamfen da ya halarta, inji rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Baba-Ahmed Ya Gargadi Yan Najeriya Akan Su Guje Wa Yan Takara Masu Nuna Kabilanci da Addini a Zaben 2023

Kungiyar Inyamurai ta fusata, ta nemi Atiku ya nemi gafarar 'yan Kudu
Kungiyar Inyamurai Ta Ohanaeze Ta Bukaci Atiku Ya Nemi Afuwa Kan Kalamansa da Ka Iya Raba Kai | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Kungiyar ta kuma nemi ya lashe aman da ya yi na cewa, 'yan Arewa kada su zabi Bayarbe ko Inyamuri, su zabe shi tunda shi dan Arewa ne, inda kungiyar tace hakan zai iya raba kan 'yan Najeriya.

Dama haka Atiku ya kudurta a ransa, inji shugaban Ohanaeze

Da yake martani ga batutuwan Atiku a wata hira, shugaban kungiyar Ohanaeze, Alex Ogbonnia ya ce, maganar ta Atiku ta nuna abin da ya kudurta a ransa ne game da kasar nan, rahoton Punch.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma bayyana cewa, bayanin Atiku ya saba da da'awar da yake yi na son ganin ya dunkula kan 'yan Najeriya.

A ceewar Ogbonnia:

"Wannan magana ne mai tada hankali dake fitowa daga bakin tsohon mataimakin shugaban Najeriya. Bayaninsa watakila ya bayyana gaskiyar abin da ke ransa ne game da kasar."

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya gaji, ya kamata ya koma gida, ya kama gado ya huta, inji hadimin Atiku

Maganar Atiku ta saba da tarihin Najeriya, inji shugaban Ohanaeze

A bangare guda, ya yi tsokaci da cewa, a tarihin Najeriya, an samu lokacin da 'yan Kudu suka zabi 'yan takara daga yankin Arewacin kasar nan.

A kalamansa:

"A rubuce yake cewa Inyamurai da yankin Kudu sun zabi Balewa. Sun zabi Shagari, Yar Adua da Buhari. Don haka, me yasa ba za a samu sakayyar hakan ba?"

Hakazalika, kungiyar ta shawarci Atiku da cewa, kamata ya yi ya ci gaba da kamfen dinsa ba tare da kawo batun da ya shafi kabilanci ba.

A wani labarin kuma, shugabancin kungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Legas ta bayyana goyon bayanta ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu.

Wannan batu na goyon baya na fitowa ne a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba daga bakin shugaban CAN na Legas, Rabaran Stephen Adegbite, inji rahoton jaridar Independent.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Dole PDP Ta Fito Ta Baiwa Yan Najeriya Hakuri Kan Maganganun Atiku - Wike

A nasa fahimtar, shugaban na CAN ya ce, tabbas Allah zai hukunta duk wani kirista a karkashin CAN ta Legas da ya ki goyon bayan Tinubu a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel