Da Dumi-dumi: Dole PDP Ta Fito Ta Baiwa Yan Najeriya Hakuri Kan Maganganun Atiku - Wike

Da Dumi-dumi: Dole PDP Ta Fito Ta Baiwa Yan Najeriya Hakuri Kan Maganganun Atiku - Wike

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya nuna rashin jin dadinsa kan kalaman da dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar yayi
  • Atiku ya ce dan arewa baya bukatar Bayarabe ko Inyamuri a matsayin shugaban kasa face wani dan arewa
  • Wike ya bukaci jam'iyyar PDP a kan lallai ta fito ta baiwa yan Najeriya hakuri saboda wannan furuci na dan takararta

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi kira ga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ta fito ta baiwa yan Najeriya hakuri kan kalaman da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar yayi, The Nation ta rahoto.

Atiku dai ya ce kasar Najeriya bata bukatar dan takara Bayarabe ko Ibo ya mulketa a matsayin shugaban kasa sai dai wani dan arewa.

Kara karanta wannan

Lamari Ya Dagule Bayan Atiku Yace Arewa Bata Bukatar Bayerabe Ko Ibo Ya Mulki Najeriya a 2023

Atiku da Wike
Da Dumi-dumi: Dole PDP Ta Fito Ta Baiwa Yan Najeriya Hakuri Kan Maganganun Atiku - Wike Hoto: Atiku Abubakar, Gov Nyesom Ezenwo Wike - CON
Asali: Facebook

Wike ya ce wannan furucin da ke zuwa a daidai lokacin da kasar ke tsananin bukatar hadin kai ya nuna karara cewa Atiku ba mai son adalci bane.

Ya kuma ce wannan ne dalilin da yasa tsagin Atiku basa so shugaban PDP na kasa, yayi murabus saboda basa son adalci, gaskiya da daidaito a jam’iyyar, rahoton AIT.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnan ya bayyana haken a Port Harcourt a ranar Litinin, 17 ga watan Oktoba, jim kadan bayan dawowarsa kasar daga Spain.

Ya bayyana cewa dole jam’iyyar ta gaggauta magance lamarin da kuma ba yan Najeriya hakuri idan ba haka ba mutane zasu fara kallon jam’iyyar a matsayin wacce bata da adalci da daidaito.

Atiku: Yan Arewa Na Bukatar Dan Arewa Ya Zama Shugaban Kasa Ba Bayarabe Ko Inyamuri Ba

A baya mun kawo cewa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya bayyana cewa yan arewa na bukatar wani shugaban kasa da ya fito daga yankin arewacin kasar.

Kara karanta wannan

Atiku: Yan Arewa Na Bukatar Dan Arewa Ya Zama Shugaban Kasa Ba Bayarabe Ko Inyamuri Ba

Atiku ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 15 ga watan Oktoba, a wani taron yan arewa da aka gudanar a jihar Kaduna, The Cable ta rahoto.

Yayin da yake jawabi ga taron al’ummar Hausa Fulani da dama, tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa basa bukatar dan Igbo ko bayarabe a matsayin shugaban kasa sai dai wani daga arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel