Baba-Ahmed Ya Gargadi Yan Najeriya Akan Su Guje Wa Yan Takara Masu Nuna Kabilanci da Addini a Zaben 2023

Baba-Ahmed Ya Gargadi Yan Najeriya Akan Su Guje Wa Yan Takara Masu Nuna Kabilanci da Addini a Zaben 2023

  • Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar LP. Yusuf Baba-Ahmed, ya gargadi yan Najeriya a kan su guji wasu yan siyasa gabannin 2023
  • Baba-Ahmed ya bukaci al’ummar kasar da kada su zabi yan siyasa masu fakewa da addini da kabilanci a yayin kamfen dinsu
  • Dan siyasar ya shawarci matasa da su mallaki katunan zabensu don zabar yan takarar da suka cancanta tare da fatattakar masu mulkin kama karya

Niger - Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Yusuf Baba-Ahmed, ya yi kira ga yan Najeriya da su guji zabar yan siyasa da ke kada gangar kabilanci da addini a yayin kamfen.

“Ina mai umurtanku da ku yi watsi da irin wadannan mutane dannan ku zabi inganci, cancanta, halayya, daidaito, adalci da gaskiya domin ceto Najeriya daga durgushewa,”

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Atiku Ya Shilla Turai Ana Tsaka da Gangamin Yakin Neman Zabe

...... A cewarsa.

Baba-Ahmed
Baba-Ahmed Ya Gargadi Yan Najeriya Akan Su Guje Wa Yan Takara Masu Nuna Kabilanci da Addini a Zaben 2023 Hoo: dailypost.ng
Asali: Twitter

Baba-Ahmed ya yi kiran ne a wani taro da masu ruwa da tsaki a garin Minna, babban birnin jihar Neja, a ranar Asabar, 15 ga watan Oktoba, jaridar Punch ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce duk dan takarar da ke amfani da banbancin addini ko kabila a matsayin dabara wajen kamfen dinsa baya nufin kasar nan da alkhairi.

Dan takarar mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa jam’iyyun PDP da APCsun shafe tsawon shekaru 24 suna mulkin kama karya a kasar.

Ya kuma bayyana cewa lokaci yayi da yan Najeriya zasu tashi tsaye domin kwato kasar daga halaka.

Ya bukaci matasa da su tabbata sun karbi katunan zabensu sannan su fito kwansu da kwarkwata don fatattakar yan siyasa da suka yi watsi dasu amma kuma suke son ci gaba da mulkarsu.

Kara karanta wannan

Kamfen 2023: 'Yan A Mutun APC Na Bin Gida-gida Don Tallata Dan Takararsu Bola Tinubu A Wata Jahar Arewa

Baba-Ahmed ya kara da cewa:

“Ku yi waje da yan siyasar da basu da abun da zasu yi amfani dashi wajen rufe karairayinsu da rashin dabarun magance tarin matsalolin da Najeriya ke fuskanta.
“Za su bi ta kowani hanya don haddasa rudani, ta hanyar amfani da banbancin addini da kabilanci, don haka kada yan Najeriya su fada tarkonsu.”

Da Dumi-dumi: Dole PDP Ta Fito Ta Baiwa Yan Najeriya Hakuri Kan Maganganun Atiku - Wike

A wani labarin, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi kira ga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ta fito ta baiwa yan Najeriya hakuri kan kalaman da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar yayi, The Nation ta rahoto.

Atiku dai ya ce kasar Najeriya bata bukatar dan takara Bayarabe ko Ibo ya mulketa a matsayin shugaban kasa sai dai wani dan arewa.

Wike ya ce wannan furucin da ke zuwa a daidai lokacin da kasar ke tsananin bukatar hadin kai ya nuna karara cewa Atiku ba mai son adalci bane.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Dole PDP Ta Fito Ta Baiwa Yan Najeriya Hakuri Kan Maganganun Atiku - Wike

Asali: Legit.ng

Online view pixel