Jerin Gwamnoni 4 da ke Tare da Atiku, Suka Shirya Yaki da Wike da Mutanensa a PDP
- Rigimar da ta bijirowa jam’iyyar hamayya ta PDP tun bayan zaben ‘dan takara ba ta zo karshe ba
- Gwamnan Ribas Nyesom Wike yana tare da wasu gwamnonin jihohi da manyan PDP a bangarensa
- A gefe guda akwai Gwamnonin da ke goyon bayan Atiku Abubakar da shugaban jam’iyya na kasa
Abuja - Wani rahoto da ya fara bayyana a jaridar The Nation, ya nuna wasu gwamnoni sun ja daga da bangaren Nyesom Wike a jam’iyyar PDP.
Wadannan gwamnonin jihohi ba su goyon bayan Gwamna Nyesom Wike da mutanensa da suke adawa da shugabancin Iyorchia Ayu a jam’iyya.
Rahoton yace lamarin har ya kai gwamnonin suna yi wa Atiku Abubakar barazanar watsi da shi a 2023 idan har ya biyewa bukatun Wike da mutanensa.
Su wanene wadannan gwamnoni da ke goyon bayan Atiku Abubakar:
1. Godwin Obaseki
Gwamna Godwin Obaseki bai tare da Nyesom Wike duk da sun fito daga yanki daya. Ana tunanin Atiku Abubakar ya yi tasiri wajen shigowarsa PDP daga APC a 2020.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A halin yanzu ana rikici tsakanin Gwamna Godwin Obaseki da bangaren Dan Orbih a PDP ta reshen jihar Edo. Orbih da mutanensa suna tare da bangaren Nyesom Wike.
2. Ahmadu Fintiri
Mai girma gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri yana cikin manyan magoya bayan Atiku Abubakar. Akasin Obaseki, ba a taba jinsa yana rigima da Wike ba.
3. Duoye Diri
Shi ma Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri bai cikin mutanen Wike duk da yana yankin kudu maso kudancin Najeriya, kuma da farko ya nuna yana tare da takwaransa.
Diri yana cikin gwamnonin kudancin Najeriya da aka tura domin su lallabi Nyesom Wike.
4. Darius Ishaku
Shi ma Gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba yana goyon bayan takarar Atiku Abubakar. Tun can tsohon mataimakin shugaban kasar yana da karfi a yankin.
Darius Ishaku ya yi aiki da Wike a lokacin suna Ministoci a gwamnatin Goodluck Jonathan. A lokaci daya dukkaninsu suka ajiye aiki, suka yi takarar gwamna a 2015.
Kuna sane cewa gwamnonin da ke tare da Wike su ne Seyi Makinde (Oyo), Samuel Ortom (Benue), Okezie Ikpeazu (Abia), sai kuma Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu).
Ina tare da Atiku - Nyesom Wike
A makon jiya aka ji Nyesom Wike ya tabbatar da cewa bai da matsala da takarar da Atiku Abubakar yake yi, yace yana goyon bayan Atiku/Okowa a 2023.
Nyesom Wike ya sha sharadi, yace sai an yi waje da Iyorchia Ayu domin yana ganin ba adalci ba ne a hana ‘Yan Kudu tikitin takara da shugabancin jam'iyya.
Asali: Legit.ng