Duk Jam'iyyar Dake Takara Da APC a Legas 'Batawa Kanta Lokaci Take, Wike

Duk Jam'iyyar Dake Takara Da APC a Legas 'Batawa Kanta Lokaci Take, Wike

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya yiwa shugabannin PDP a Legas kalmar hannunka mai sanda
  • Wike wanda tsohon dan takaran shugaban kasa karkashin PDP ne yana goyon bayan APC a Legas
  • Masu sharhi kan lamuran siyasa dai na cewa da yiwuwan WIke a karshe ya sauya sheka APC

Legas - Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya bayyana cewa duk jam'iyyar dake takara da jam'iyyar All Progressives Congress APC a jihar Legas tana batawa kanta lokaci ne.

Gboyega Akosile, Sakataren yada labaran gwamnan Legas ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita ranar Talata.

Akosile ya ruwaito Wike da cewa gwamna Sanwo-Olu na jihar Legas agogo sarkin aiki ne.

Ya rubuta cewa:

"Duk jam'iyyar dake takara da APC a jihar Legas na batawa kanta lokaci ne. Sanwo-Olu ma'aikaci ne - Gov Nyesom Wike."

Kara karanta wannan

Jami'in Soja Ya Arce Da Kudin Kwamanda N36m A Jihar Rivers, An nemesa an rasa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamna Wike Ya Bayyana Goyon Bayan Kudirin Tazarcen Gwamnan APC

Nyesom Wike, ya bayyana goyon bayansa kan kudirin tazarcen takwaransa na jihar Legas, Babajide Sanwo Olu.

Wike yace da duk da cewa ba jam'iyyarsa daya da Sanwo-Olu, Shi shaida ne gwamnan na Legas ya yi aikin kwarai a jihar.

Shin Wike na kokarin sauya sheka ne?

Rikicin dake gudana tsakanin gwamnoni biyar dake jam'iyyar PDP da shugaban jam'iyyar Iyorchia Ayu ya ki ci, ya ki cinyewa.

Gwamnonin da aka yiwa lakabi da G5 sun ce sai Ayu ya sauka zasu goyi bayan dan takaran shugaban kasan jam'iyyar, Atiku Abubakar.

Gwamnonin sun hada da Nyesom Wike na Rivers, Samuel Ortom na Benue, Ikezie Ikpeazu na Abia, Seyi Makinde na Oyo da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel