Da Duminsa: Gwamna Wike Ya Bayyana Goyon Bayan Kudirin Tazarcen Gwamnan APC
- Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas kuma jigon jam’iyyar PDP na kasa, ya bayyana goyon bayan tazarcen Gwamna Sanwo Olu na jam’iyyar APC a Legas
- Babban sakataren yada labarai na Gwamna Sanwo-Olu, Gboyega Akosile ne ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Talata
- Wannan abun mamakin na zuwa ne duk da jam’iyyar PDP tana da ‘dan Takarar Gwamna a jihar Legas mai suna Olajide Adediran wanda aka fi sani da Jandor
Legas - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana goyon bayansa kan kudirin tazarcen takwaransa na jihar Legas, Babajide Sanwo Olu.
Jaridar Punch ta rahoto cewa, wannan na kunshe ne a takardar da sakataren yada labarai na Gwamna Sanwo-Olu, Gboyega Akosile ya fitar a ranar Talata.
“Labari da Duminsa: Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya bayyana goyon bayansa kan kudirin tazarcen Babajide Sanwo-Olu. Karin bayani na nan tafe.”
- Akosile ya rubuta.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wannan bayyana goyon bayan na zuwa ne duk da jam’iyyar PDP wacce ita ce ta Gwamna Wike tana da ‘dan takara a jihar Legas mai suna Olajide Adediranw wanda aka fi sani da Jandor.
Kamar yadda aka sani, rikicin cikin gida na cigaba da kamari a jam’iyyar PDP inda Wike da wasu gwamnoni suka ware kansu kuma suke terere ga jam’iyya.
Wannan na zuwa ne duk daga cikin tada kayar bayan da Wike yake yi kan cewa shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu dole yayi murabus.
2023: Nan Babu Dadewa Wike da Tawagarsa Zasu Koma Wurin Tinubu, 'Dan APC Yayi Hasashe
A wani labari na daban, a yayin da rikicin cikin gida ke cigaba da kamari a jam'iyyar PDP ta hamayya, tsagin Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas sun janye daga tawagar gangamin zaben shugabancin kasa.
Duk da Gwamna Wike, shugaban tsagin, yace ba zai bar jam'iyyar PDP ba, akwai hasashen dake nuna cewa shi da mukarrabansa zasu yi wa Tinubu aiki.
Ana tsaka da wannan hasashen, Legit.ng ta zanata da Ahmad Abba Dangata, tsohon mai neman takarar shugaban matasa na kasa na jam'iyyar APC wanda ya bayyana tunaninsa kan wannan cigaban da sauran abubuwan da suke yawo a jam'iyyar.
Asali: Legit.ng