Mutum 18 Sun Jigata, An Rasa Rai 1 a Mummunan Arangamar Matasan APC da PDP a Zamfara

Mutum 18 Sun Jigata, An Rasa Rai 1 a Mummunan Arangamar Matasan APC da PDP a Zamfara

  • Yan sandan jihar Zamfara sun tabbatar da halaka mutum 1 tare da jigata wasu 18 sakamakon arangamar da aka yi tsakanin ‘yan daban siyasan APC da na PDP
  • Duk da kowacce daga cikin jam’iyyun na zargin abokiyar hamayyarta da kai mata farmaki, ’yan sanda sun ce tuni aka fara bincike
  • APC tace yaran ‘dan takarar gwamnan jihar ne suka kai musu harin yayin da suke tsaka da al’amuran siyasarsu a Gusau dake Zamfara

Gusau, Zamfara - Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara tace an tabbatar da mutuwar mutum daya yayin da wasu 18 suka jigata sakamakon arangama tsakanin kungiyoyin matasa biyu a jihar.

Taswirar Zamfara
Mutum 18 Sun Jigata, An Rasa Rai 1 a Mummunan Arangamar Matasan APC da PDP a Zamfara. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Kamar yadda ‘yan sandan suka bayyana, kungiyoyin da lamarin ya shafa ana zargin na matasan APC da PDP ne a jihar, jaridar TheCable ta rahoto.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Dakile Harin ‘Yan Bindiga, Sun Sheke 2, Wasu Sun Jigata

Muhammad Shehu, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Gusau, babban birnin jihar a ranar Litinin.

“Binciken datsan-datsan aka fara kan lamarin wanda makasudinsa shine zakulo masu laifin tare da hukuntasu.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Shehu yace.

Jam’iyyar APC a jihar Zamfara a ranar Asabar ta zargi cewa ‘yan daban PDP ne suka kaddamar da wani hari a kansu.

“Abun takaici ne da taba zuciya yadda aka kai farmakin da makamai wanda ‘yan daban PDP ne suka kai.

- Takardar da Yusuf Idris, sakataren yada labarai na jam’iyyar APC ya fitar a Gusau ta bayyana.

“‘Yan daban sun zo a matsayin yaran ‘dan takarar gwamna kuma sun fara harbin matasan da basu ji ba, basu gani ba dake aikin tsaftace yankin GRA a Gusau wanda ake yi wata wata.

Kara karanta wannan

Katsina: ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutum 18 Yayin da Suka Bankado Harin ‘Yan Bindiga

“Muna kira ga mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu balle wadanda ‘yan daban suka hargitsa. Muna kira ga gwamnatin jihar da hukumomin tsaro da su hanzarta tsamo wadanda suka aikata laifin kuma su hukuntasu domin gujewa aikin daukar fansa.”

A yayin martani kan zargin, PDP tace Dauda Lawal Dare, ‘Dan takarar kujerar gwamna taro kadai yayi da masu sauya sheka daga kananan hukumomi 14 na jihar a ranar Asabar.

Kamar yadda Mukhtar Lugga, mataimakin shugaban PDP na Zamfara ya bayyana, bayan taron sun karba masu sauya sheka 50 daga kowanne daga cikin kananan hukumomi 14 na jihar.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, sai dai ya zargi cewa an kai wa wasu matasan PDP hari a yayin taron inda ya nada da cewa an harba wasu magoya bayansu biyu a gaban ofishin kamfen din ‘dan takarar gwamnan dake Gusau.

Lugga tace zasu binciki zargin arangamar da magoya bayansu kuma zasu dauka mataki inda ya dace.

Kara karanta wannan

Zamfara: ‘Yan sanda Sun Kama Mota Dankare da Kayan Abinci da Miyagun Kwayoyi Za a Kaiwa ‘Yan Bindiga

Zamfara: Sunayen Kananan Hukumomi 3 da Matawalle ya Garkame, Ya Hana Tarukan Siyasa

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Zamfara a ranar Juma’a ta sanar da rufe kananan hukumomin Anka, Bukkuyum da Gummi a jihar sakamakon hauhawar rashin tsaro da farmakin ‘yan bindiga a yankunan.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, sanarwar rufe kananan hukumomin yana kunshe ne a wata takarda da kwamishinan yada labarai, Alhaji Ibrahim Dosara ya fitar a ranar Juma’a a Gusau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel