Katsina: ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutum 18 Yayin da Suka Bankado Harin ‘Yan Bindiga

Katsina: ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutum 18 Yayin da Suka Bankado Harin ‘Yan Bindiga

  • Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah ya tabbatar da ceto wasu mutum 18 da masu garkuwa suka sace a Katsina
  • Ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa daga kauyen Gatakawa dake karamar hukumar Kankara kan cewa ‘yan bindiga sun kai hari
  • Jami’an ‘yan sandan sun dira kauyen inda suka yi artabu da ‘yan bindigan, sun halaka biyu daga ciki tare da raunata wasu masu yawa

Katsina - Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina tace ta bankado wani harin ‘yan bindiga a yankin Gatakawa dake karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isah yace jami’an sun ceto mutum 18 da aka yi garkuwa dasu, jaridar TheCable ta rahoto.

Taswirar Katsina
Katsina: ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutum 18 Yayin da Suka Bankado Harin ‘Yan Bindiga. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Isah yayi bayanin cewa, a ranar 12 ga watan Oktoba wurin karfe 1 na dare, rundunar ta samu kiran gaggawa kan cewa ‘yan bindiga masu yawa sun kutsa kauyen inda suke ta harbi babu kakkautawa.

“Bayan samun rahoton, DPO din Kankara ya jagoranci jami’ai zuwa yankin kuma sun yi artabu da ‘yan ta’addan.”

- Isah yace.

“Tawagar cike da nasara ta dakile harin ‘yan bindigan inda ta hana su cimma mummunan burinsu tare da ceto wadanda suka yi garkuwa dasu.”

Sai dai, ya bayyana cewa an rasa rayukan mutum biyu a wannan farmakin.

“A yayin duba inda lamarin ya faru, an samu babura biya da shanu biyu. Sai dai cike da takaici an rasa rayukan mutum biyu kuma daya daga cikin wadanda ake zargin ya jigata.
“Ana tsoron da yawa daga cikin ‘yan bindigan an halaka su ko kuma sun arce daga wurin da raunikan bindiga. Ana cigaba da binciken.”

Zamfara: ‘Yan sanda Sun Kama Mota Dankare da Kayan Abinci da Miyagun Kwayoyi Za a Kaiwa ‘Yan Bindiga

A wani labari na daban, Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara sun kama mota dankare da kayan abinci da za a kaiwa ‘yan bindigan dake da maboya a Dangulbi a karamar hukumar Maru ta jihar, jaridar Premium Times ta rahoto.

A wata takarda da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu yasa hannu a ranar Laraba, ‘yan sandan sun damke mutum takwas dake kai wa ‘yan bindiga bayanai, harsasai carbi 250 na AK47 da shanun sata 47.

Asali: Legit.ng

Online view pixel