‘Yan Sanda Sun Dakile Harin ‘Yan Bindiga, Sun Sheke 2, Wasu Sun Jigata

‘Yan Sanda Sun Dakile Harin ‘Yan Bindiga, Sun Sheke 2, Wasu Sun Jigata

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da harbe wasu ‘Yan bindiga biyu da jami’anta suka yi a Idasso dake Galadima a karamar hukumar Giwa
  • Mohammed Jalige, kakakin rundunar ya sanar da cewa ‘yan bindigan sun kai farmaki ne amma ‘yan sandan suka hanzarta kai musu dauki
  • Jalige yace sun kama bindiga kirar AK49 dauke da harsasai 24 da babur daya yayin da wasu ‘yan bindiga suka jigata

Kaduna - Dubun wasu ‘yan bindiga biyu a yankin Idasso dake Kidandan ta Galadimawa a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna ta cika bayan an an bindigesu har lahira, Daily Trust ta rahoto hakan.

Taswirar Kaduna
‘Yan Sanda Sun Dakile Harin ‘Yan Bindiga, Sun Sheke 2, Wasu Sun Jigata. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da hakan a ranar Alhamis inda tace wasu daga cikin ‘yan bindigan sun tsere da raunika.

Kara karanta wannan

Katsina: ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutum 18 Yayin da Suka Bankado Harin ‘Yan Bindiga

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Mohammed Jalige ya bayyana, ‘yan bindiga da tarin yawansu sun kai farmaki amma sai suka dakilesu.

Yace bayan sun samu bayanai, rundunar ta hanzarta aikewa da jami’ai wurin domin dakile faruwar aika-aikar.

Jalige yace an samu bindiga kirar AK49 dankare da harsasai masu rai har 24 kuma an samo babur din wani ‘dan bindiga daya yayin da ya tsere.

“An ceto wani Yusuf Dahiru mai shekaru 65 da aka yi garkuwa da shi. A halin yanzu jami’an na cigaba da duba dajin domin cafke ‘yan bindigan da suka tsere.”

- Yace.

Yace kwamishinan ‘yan sanda ya yabawa sadaukarwar da jami’an suke yi a kowacce rana wurin tabbatar da zaman lafiya da lumana a jihar.

Katsina: ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutum 18 Yayin da Suka Bankado Harin ‘Yan Bindiga

Kara karanta wannan

Zamfara: ‘Yan sanda Sun Kama Mota Dankare da Kayan Abinci da Miyagun Kwayoyi Za a Kaiwa ‘Yan Bindiga

A wani labari na daban, Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina tace ta bankado wani harin ‘yan bindiga a yankin Gatakawa dake karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isah yace jami’an sun ceto mutum 18 da aka yi garkuwa dasu, jaridar TheCable ta rahoto.

Isah yayi bayanin cewa, a ranar 12 ga watan Oktoba wurin karfe 1 na dare, rundunar ta samu kiran gaggawa kan cewa ‘yan bindiga masu yawa sun kutsa kauyen inda suke ta harbi babu kakkautawa.

“Bayan samun rahoton, DPO din Kankara ya jagoranci jami’ai zuwa yankin kuma sun yi artabu da ‘yan ta’addan.”

- Isah yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel