Zamfara: Sunayen Kananan Hukumomi 3 da Matawalle ya Garkame, Ya Hana Tarukan Siyasa

Zamfara: Sunayen Kananan Hukumomi 3 da Matawalle ya Garkame, Ya Hana Tarukan Siyasa

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da garkame kananan hukumomin Anka, Bukkuyum da Gummi sakamakon hauhawar rashin tsaro a yankunan
  • Gwamnan ya sanar da dakatar da dukkan lamurran siyasa tare da tarukan APC domin taya jama’ar yankunan alhinin abinda ke faruwa
  • Matawalle ya sanar da cewa hakan ya zama dole domin tallafawa kokarin hukumomin tsaro wurinsa dakile rashin tsaron dake cigaba da yaduwa

Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara a ranar Juma’a ta sanar da rufe kananan hukumomin Anka, Bukkuyum da Gummi a jihar sakamakon hauhawar rashin tsaro da farmakin ‘yan bindiga a yankunan.

Zamfara Map
Zamfara: Sunayen Kananan Hukumomi 3 da Matawalle ya Garkame, Ya Hana Tarukan Siyasa. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, sanarwar rufe kananan hukumomin yana kunshe ne a wata takarda da kwamishinan yada labarai, Alhaji Ibrahim Dosara ya fitar a ranar Juma’a a Gusau.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 2 za su ba 'yan banga AK-47, rundunar soji ta yi martani mai zafi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Gwamnati na sanar da rufe manyan garuruwa tara domin dakile cigaban hare-hare a wasu yankuna.
“Wadannan yankunan sun hada da Yarkofoji, Birnin Tudu m, Rini, Gora Namaye, Janbako, Faru, Kaya, Boko da Mada.
“Gwamnatin ta kara da sanar da rufe kasuwanni a Danjibga da Bagega da titin Lambar Boko, Bakura zuwa Lambar Damri da Mayanchi zuwa Daki-Takwas zuwa Gummi.
“Sauran sun hada da titin Daki Takwas zuwa Zuru, Kucheri zuwa Bawaganga zuwa Wanke, Magami zuwa Dangulbi da Gusau zuwa Magami.
“An dauka wadannan mayakan ne domin taimakawa kokarin jami’an tsaro wurin kakkabo masu laifi a wadannan yankunan.”

- Gwamnatin tace.

Gwamna Bello Matawalle ya kara da umarnin dakatar da dukkan tarukan APC da siyasa a matsayin hanyar jaje da tausayawa wadanda lamarin ya ritsa dasu.

“Masu ruwa da tsakin da aka bayyana taron APC na ranar Juma’a ana shawartarsu da su dakata har sai an bayyana musu sabuwar ranar taron.

Kara karanta wannan

Yadda Budurwa Ta Kashe Saurayinta Da Wuka Cikin Dare Kusa Da Dakin Hotel

“Har ila yau, gwamnati ta dakatar da dukkan lamurran siyasa har sai baba ta gani.
“A haramta tarukan siyasa a gidajen jama’a.”

- Dosara ya kara da cewa.

Gwamnatin jihar tace an yanke wannan hukuncin ne domin magance halin da ake ciki kafin yayi kamari.

Hakazalika gwamnatin jihar ta umarci hukumomin tsaro da su yi maganin duk wanda suka kama yana take dokokin da aka saka.

Legit.ng Hausa ta samu zantawa da Injiniya Bello Muhammad ‘dan asalin Boko amma mazaunin Gusau, ya tabbatar da cewa hakan ce kawai mafita domin farmakin da ake kaiwa yankunan ya kazanta.

”A nawa hangen hakan ne kawai mafita saboda harin da ake kaiwa yankunan yayi muni.
”Wasu duk sun tsere gudun hijira sakamakon tsoron mugayen mutanen nan. Ban san yawan ‘yan uwana da na rasa ba.
”Ko da lamurran ‘yan bindigan suka fara lafawa mu a can basu lafa ba. Yanzu ne ma suke tashe.”

Kara karanta wannan

2023: Daruruwan 'Ya'Yan APC a Mazabar Gwamnan Arewa Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

- Muhammad ya bayyana.

Ya kara da bayyana cewa hukumomin tsaro suna kokarinsu don haka ya zama dole gwamnati ta dauka irin wannan mayakan don taimaka musu.

Zamfara: ‘Yan sanda Sun Kama Mota Dankare da Kayan Abinci da Miyagun Kwayoyi Za a Kaiwa ‘Yan Bindiga

A wani labari na daban, Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara sun kama mota dankare da kayan abinci da za a kaiwa ‘yan bindigan dake da maboya a Dangulbi a karamar hukumar Maru ta jihar, jaridar Premium Times ta rahoto.

A wata takarda da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu yasa hannu a ranar Laraba, ‘yan sandan sun damke mutum takwas dake kai wa ‘yan bindiga bayanai, harsasai carbi 250 na AK47 da shanun sata 47.

Asali: Legit.ng

Online view pixel