Rarara Ya Caccaki Ganduje A Sabuwar Waƙa Da Ya Fitar, Lamarin Ya Haifar Da Cece-Kuce A Soshiyal Midiya

Rarara Ya Caccaki Ganduje A Sabuwar Waƙa Da Ya Fitar, Lamarin Ya Haifar Da Cece-Kuce A Soshiyal Midiya

  • Cece-kuce ya barke a shafukan sada zumunta na intanet a yayin da Dauda Kahutu Rarara ya soki Gwamna Ganduje a sabuwar waka ya kira shi hankaka
  • Rarara ya kuma tabbatar da cewa har yanzu shi ɗan APC ne kuma yana tare da Tinubu/Shettima amma ba ya goyon bayan Dr Nasiru Gawuna ɗan takarar gwamnan APC a Kano da Ganduje ke fatan ya gaje shi
  • Mawakin siyasan da ya shahara wurin yi wa Shugaba Muhammadu Buhari waka ya yi ikirarin cewa Ganduje ya bada umurnin a cire sunansa daga kwamitin kamfen din takarar shugaban kasa

Kano - Fitaccen mawakin siyasa nan na Hausa Dauda Kahutu Rarara, wanda ya yi fice wajen yi wa Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya waka, ya saki sabuwar waka inda ya soki Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Lallai Na Yi Dace Wajen Zaben Okowa Matsayin Mataimaki Na, Atiku

Rarara, wanda shine shugaban kungiyar siyasa ta Kannywood, 13X13, ya kasance cikin masu yaba wa Ganduje kuma ya bada goyon baya a manyan zaben 2015 da 2019.

Rarara
Rarara Ya Caccaki Ganduje A Sabuwar Waƙa Da Ya Fitar, Lamarin Ya Haifar Da Cecec-Kuce A Soshiyal Midiya. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa mawakin baya goyon bayan Dr Nasiru Yusuf Gawuna, ɗan takarar gwamna na APC a Kano, maimakon haka, ya bayyana goyon baya ga Sha'aban Ibrahim Sharada na Action Democratic Party, ADP.

Amma ya jaddada cewa har yanzu shi ɗan APC ne kuma yana goyon bayan takarar shugaban kasa na Tinubu/Shettima.

Rarara ya kira Ganduje Hankaka a sabuwar waka

Amma, cikin sabuwar wakar da ya fitar a ranar Laraba don yi wa Tinubu kamfen, Rarara ya tabbatar da rikicinsa da Ganduje kuma ya bayyana gwamnan a matsayin 'Hankaka', ma'ana mutum mai fuska biyu.

Rarara kuma ya zargi Ganduje da daƙile saka sunansa a kwamitin kamfen din shugaban kasa na APC.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Wani Matashi Ya Naushi Abokinsa, Ya Faɗi Ya Mutu a Birnin Kano

A cikin wakar, Rarara ya ce:

"Ka ce su cire suna na kuma na ji, amma ban taba cewa a saka suna na ba. Na san dukkan tarurrukan da ka ke yi. Za mu bada gudunmawarmu ga Tinubu ba tare da muna wata tawaga ba. Kai hankaka ne kuma za mu nuna maka mune gwanayen waka....".

Martanin masu amfani da dandalin sada zumunta kan sukar da Rarara ya yi wa Ganduje a waka

Mutane sun bayyana mabanbantan ra'ayoyi game da batun wasu na cewa fadar cikin gida ne.

Wasu sun ce Rarara ya saba sukar duk wani wanda tasu ba ta zo ɗaya ba, suna zargin ya yi wa wasu da suka yi sanadin shahararsa.

Aminu Kutama a Twitter ya ce:

"Rarara ya kira Shekarau 'Ɓarawo da Duna', yan adawarsa sun yi murna. Ya kira Kwankwaso 'Tsula da Jan Biri', abokan hammayarsa suma sun yi dariya. Yanzu, ya kira Ganduje "Hankaka". Ya zaga kowa kuma lokaci ya yi da ya kamata a dena wannan rashin mutuncin!."

Kara karanta wannan

Sanatan Kano Ya Bayyana Ainahin Wanda Osinbajo Yake Goyon Baya A Zaben Shugaban Kasa Na 2023

Ya kara da cewa wata rana, Idan Buhari ya sauka daga mulki, Rarara zai zage shi.

Kwankwaso's Twitter ya ce:

"Wannan karon Rarara ne da Ganduje, yana kiran Ganduje Hankaka."

Wani kai amfani da Twitter, Adam Abdul ya ce:

"Wani mawakin mai suna Dumbulun ya zagi Rarara. Amma Rarara ya tafi ya rama kan Ganduje. Shine ainihin hankakan ba Ganduje ba. Amma wakar da dadi."

Bashir Abdullahi El-bash a Facebook ya ce:

"Ina tsoron ranar da matasa a Kano za su yi wa Rarara duka saboda zagin shugabannin mu. Shine ainihin hankakan yana ta yawo daga wannan ɗan takarar zuwa wancan."

Abdullahi Umar Bichi ya ce:

"Tinubu zai zo Kano mako mai zuwa. Tunda ka ce za ka iya bashi gudunmawa ba tare da nadi ba, ka gwada zuwa wurin taron a ranar mu gani."

Ban san haka Buhari ke da farin jini ba wurin al'umma - Rarara

Kara karanta wannan

Rikici: An farmaki hadimin Ganduje a Kano, ya ce 'yan Kwankwasiyya ne suka sace wayarsa

Dauda Kahutu Rarara ya shahara sosai saboda yi wa Shugaba Muhammadu Buhari wakoki na yabo.

A makon da ta gabata, ya wallafa sako a dandalin sada zumunta inda ya bukaci magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari su tallafa masa da Naira dubu dai-dai domin ya fitar da sabuwar album dinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel