Ban yi Zaɓen Tumun Dare Ba Wajen Zaɓar Okowa a kan Wike – Atiku

Ban yi Zaɓen Tumun Dare Ba Wajen Zaɓar Okowa a kan Wike – Atiku

  • Dan takarar kujerar shugaban kasa ya jaddada cewa ya yi dacen zaben Okowa matsayin mataimakinsa
  • Atiku ya taya gwamnan na Delta murnar samun lamban girmamawa daga wajen shugaba Buhari
  • Har yanzu rikici na cigaba da gudana tsakanin bangaren gwamna Wike da Alhaji Atiku

Abuja - Atiku Abubakar Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP mai adawa yace bai yi zaɓen tumin dareba a zabar dan takarar mataimakinsa Mista Ifeanyi Okowa.

Ya bayyana hakan ne bayan karramarwa da shugaban kasa yai masa da lambar yabo ta (CON), a cikin wani takaicacceyar wallafa da ya yi a shafinsa na Tuwita, inda ya taya gwamnan jihar Delta murnar samun lambar girman.

Ya ce,

“Karramawar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa Gwamna Ifeanyi Okowa shaida ce ta dacen da na yi wajen tsayar dan takararar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023."

Kara karanta wannan

Sanatan Kano Ya Bayyana Ainahin Wanda Osinbajo Yake Goyon Baya A Zaben Shugaban Kasa Na 2023

A madadin iyalai na, da tawagarmu da magoya bayanmu, ina mai cewa na taya ka murna."
Atiku
Ban yi Zaɓen Tumun Dare Ba Wajen Zaɓar Okowa a kan Wike – Atiku
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Okowa na daya daga cikin mutane sama da 400 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karrama da lambar girmamawa ta kasa.

Wasu ‘yan jam’iyyar PDP sun caccaki Atiku kan zaben Okowa a kan Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas wanda ya zo na biyu a zaben fidda gwanin shugaban kasa na jam’iyyar PDP.

An yi imanin rashin zaɓar Wike da ɗauko Okowa na daga cikin abubuwan da suka haddasa rigingimun yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar PDP.

Wike, gwamnoni hudu da wasu jiga-jigan jam’iyyar sun kaurace wa kaddamar da yakin neman zaben Atikun a Uyo, jihar Akwa Ibom a ranar Litinin din nan da ta gabata.

Kara karanta wannan

An Nemi ‘Dan Tsohon Shugaban Najeriya ya zama Mataimakin Peter Obi, Ya ki Yarda

Zan Tabbatarwa 'Yan Najeriya Tsaro Kafin Na Sauka Daga Mulki, Buhari Ya jaddada

A wani labarin daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jaddada aniyarsa tabattarwa da ‘yan Najeriya danka mulki ga wanda zai gaje shi ba tare da wata matsalar tsaro ba kamar yadda ya bayyana a bikin bayar da lambar girma ga wasu ‘yan kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel