Sanatan Kano Ya Bayyana Ainahin Wanda Osinbajo Yake Goyon Baya A Zaben Shugaban Kasa Na 2023

Sanatan Kano Ya Bayyana Ainahin Wanda Osinbajo Yake Goyon Baya A Zaben Shugaban Kasa Na 2023

  • Gabannin zaben 2023, Sanata Kabiru Gaya ya ce mataimakin shugaban kasa Osinbajo na goyon bayan takarar Tinubu karkashin inuwar APC
  • Gaya yace babu gaskiya a batun ware Osinbajo daga tawagar kamfen din shugaban kasa na jam’iyyar APC
  • Sanatan ya kuma bayyana cewa hatta Tinubu da kansa ya ziyarci Osinbajo don neman goyon bayansa bayan ya mallaki tikitin jam’iyyar mai mulki

Kano Sanata Kabiru Gaya ya tabbatar da cewar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo suna aiki kai da fata.

Sanatan ya ce bayan Tinubu ya bayyana a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki, ya ziyarci Osinbajo a gidansa sannan ya nemi ya goya masa baya.

Osinbajo da Tinubu
Sanatan Kano Ya Bayyana Ainahin Wanda Osinbajo Yake Goyon Baya A Zaben Shugaban Kasa Na 2023 Hoto: Professor Yemi Osinbajo, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa Sanata Gaya ya kara da cewa sabanin rade-radin da ke yawo, ba a mayar da mataimakin shugaban kasar saniyar ware ba a wajen kafa tawagar yakin neman zaben takarar shugabancin APC.

Kara karanta wannan

Akwai Adalci a PDP Sabanin APC: Gwamna Tambuwal Ya Bayyana Bambancin Manyan Jam’iyyun Siyasar Kasar 2

Gaya ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ni mamba ne a tawagar kamfen din Tinubu, don haka batun ware wani babu shi. Hatta shugaban kasa yace yana so Osinbajo ya kasance tare da shi wajen gudanar da harkokin kasar nan don tabbatar da mika mulki cikin sauki.
“Babu wani abu mai kama da mayar da Osinbajo saniyar ware saboda bayan zaben fidda gwani, muna a gidan Osinbajo lokacin da Tinubu ya zo sannan yace yana neman goyon bayanmu. Mun shafe tsawon awa biyu muna tattaunawa. Suna aiki tare. Bai kamata siyasa ya rabamu ba.”

Gaya wanda ya zanta da manema labarai a Kano ya jadadda cewa Osinbajo na tare da takarar shugabancin dan takarar shugaban kasa na APC.

Ya nuna yakinin cewa APC za ta lashe zabe a jihar Kano, inda ya yoi hasashen cewa NNPP zata zo ta biyu sannan PDP ta uku, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Ba Zai Yuwu Mu sha Kaye a 2023: Aisha Buhari Tayi Muhimmiyar Ganawa da Matar Tinubu

Ku Fada Wa Masu Neman Canji a Najeriya Su Rufe Bakunansu, Tinubu Ga Jirgin Kamfen Mata

A wani labarin, mun ji cewa mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar APC, Bola Tinubu, ya nemi matan jam'iyyar su gaya wa yan Najeriya dake son canjin gwamnati, "Su rufe bakinsu."

Jaridar The Cable ta tattaro cewa Tinubu ya faɗi haka ne a wurin kaddamar da tawagar kamfen APC ta mata ranar Litinin a Abuja.

Tinubu yace mutanen da ke neman canji sun manta halin da kasar nan ke ciki kafin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya karɓi mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel