Ban san haka Buhari ke da farin jini ba wurin al'umma - Rarara
- Fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya ce ya yi matukar mamakin gano cewa ashe kaunar da talakawa ke yi wa Shugaba Buhari ta wuce yadda ya ke tsammani
- Rarara ya yi wannan furucin ne sakamakon adadin kudin da ya ga 'yan Najeriya sun tara masa bayan ya nemi mutane su bayar da N1,000 domin ya yi wa Buhari sabbin wakoki
- Duk da cewa bai bayyana adadin kudin da aka tara ba kawo yanzu, Rarara ya ce cin mutunci ne a ce N70m kacal aka tara cikin kwanaki uku don yiwa muhimmmin mutum kamar Shugaba Buhari waka
Dauda Kahutu Rarara ya shahara sosai saboda yi wa Shugaba Muhammadu Buhari wakoki na yabo.
A makon da ta gabata, ya wallafa sako a dandalin sada zumunta inda ya bukaci magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari su tallafa masa da Naira dubu dai-dai domin ya fitar da sabuwar album dinsa.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe mahaifi, sun yi awon gaba da ɗansa a Katsina
Na sha mamaki, ban taba sanin haka Buhari ke da farin jini ba a cewar mawakin bayan ganin irin adadin kudin da aka tara masa.
Rarara ya ce ya gaji da jin maganganun da mutane ke yi a kan wakar da zai fitar inda zai lissafo ayyuka fiye da 192 da gwamnatin Buhari ta aiwatar a sassan kasar nan.
Da ya ke hira da Daily Trust a Kano, Rarara ya ce ya yanke hukuncin fitar da wakokin ne saboda ikirarin da wasu ke yi na cewa 'yan Najeriya sun juya wa Shugaba Muhammadu Buhari baya.
Rarara bai ambaci adadin kudin da ya samu ba a halin yanzu amma ya ce raini ne hasashen da wasu ke yi na cewa Naira miliyan 70 aka tara masa kawo yanzu.
DUBA WANNAN: Gana ya san zai mutu, ya nada wanda zai gaje shi
"Cewa Naira miliyan 70 aka tara domin mutum mai muhimmanci kamar Shugaba Muhammadu Buhari ma ai cin fuska ne, mutane ma suna son bayar da fiye da N1000 amma mu na fada musu dubu dayan kawai muke bukata. Bayan sun bayar da dubu dayan za su kuma nemi suyi kari. Ban taba ganin wani shugaba da mutane ke kauna kamar shi ba," in ji shi.
Ya kara da cewa bai riga ya sanar da duniya adadin kudin da al'umma suka tara ba domin yi wa Shugaba Buhari sabbin wakokin yabon.
"Nan gaba za mu fada wa duniya abinda muka tara domin yi wa Shugaba Buhari wakar. Za mu kira taron manema labarai mu shaida wa duniya abinda muka samu kuma mu shaidawa 'yan adawa da ke yada karya cewa an dena yayin Buhari cewa har yanzu talakawa na kaunar sa," in ji shi.
Wasu 'yan Najeriya sun soki matakin da Rarara ya dauka na cewa mutane su tara masa kudi ya yi wa Buhari waka domin nuna wa duniya cewa har yanzu suna kaunar shi.
A wani rahoton daban, kun ji cewa Tsohon gwamnan jihar Adamawa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Mista James Ngillari, ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Shugaban jam'iyyar APC na jihar Adamawa, Alh. Ibrahim Bilal, ne ya tabbatar da hakan a ranar Asabar a garin Yola kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng