Zaben 2023: INEC Ta Cire Mutum Miliyan 2.7 daga Rajista, Ta Bada Dalilin Yin Hakan

Zaben 2023: INEC Ta Cire Mutum Miliyan 2.7 daga Rajista, Ta Bada Dalilin Yin Hakan

  • Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmoud Yakubu ya yi bayanin inda aka kwana a rajistar masu zabe
  • Hukumar INEC mai gudanar da zabe tace ta cire duk wadanda aka samu sunansu ya fito fiye da daya
  • Mahmoud Yakubu yace har an buga 50% na katin PVC da za a rabawa wadanda suka yi sabon rajista

USA - Hukumar INEC mai gudanar da zabe a Najeriya, ta bayyana cewa ta cire sunayen mutane miliyan 2.7 daga rajistarta a shirye-shiryen 2023.

Rahoton da muka samu daga gidan talabijin Channels TV ya nuna nan da watan Nuwamba ne kuma wadanda suka yi rajista za su karbi katin PVC.

INEC tace an buga kusan rabin sababbin PVC da aka hada, amma ba a kai su inda za a raba ba. Mutane za su karbi katin su a wuraren da suka yi rajista.

Kara karanta wannan

Jam’iyyu Sun Tona 'Kullaliyar' da Ake Yi Na Canza Shugaban INEC da Birkita Zaben 2023

Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmoud Yakubu ya bayyana wannan a wajen wani taro da aka shirya a babban birnin Amurka, Washington DC.

Aikin rajistar masu kada kuri'a

“A zaben 2023, INEC tana shirye-shiryen mutane miliyan 95. Muna da masu zabe miliyan 84 yanzu, mun yi wa sababbin mutane miliyan 12 rajista.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babu wani a cikin sababbin rajistar nan da ya shiga cikin rajistar da ake da ita, muna ta aikin tacewa ne.”
Shugaban INEC
Shugaban INEC ya hadu da Jami'an Amurka Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

“Wasu mutane sun ce sun gano sunayen bogi a rajistar. Da na ji maganar, na tambayi kai na ‘wace rajistar?’
Ba mu kai ga tattara ta ba, muna goge ta ne.Ya za ayi mutum ya san rajistar da INEC ce za ta tattaro sunayen?
Wannan ba karamar magana ba ce saboda sai da ita za ayi zabe mai nagarta.” - Farfesa Mahmud Yakubu

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida: Ba Za Mu Sake Yarda Da Wani Zabe Na 'Inconlusive' Ba A Kano

Jaridar Sun ta rahoto Farfesa Yakubu yana cewa za a fitar da sunayen sababbin mutanen da aka yi wa rajista a mazabu 8809 da ke kananan hukumomi 774.

Matsalar rashin tsaro

Da yake jawabi a kasar ta Amurka, Yakubu yace hukumarsa na lura da sha’anin rashin tsaro da ake fama da shi har zuwa yanzu a yankunan Najeriya.

Shugaban hukumar yake cewa yanzu rashin tsaro ya fantsama zuwa wajen Arewa maso gabas, amma jami’an tsaro sun yi masu alkawari za a ga canji.

Ana so a canza shugaban INEC?

Rahoto ya zo cewa ana ikirarin za a hana amfani da na’urar BVAS a zaben badi, har ta kai ana zargin wannan ya jawo ake neman a sauke shugaban INEC.

Kungiyar CUPP tace wani Gwamnan jam’iyyar APC a Kudu maso gabashin Najeriya yake jagorantar wannan danyen aiki da ake neman yi a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel