Abba Gida-Gida: Ba Za Mu Sake Yarda Da Wani Zabe Na 'Inconlusive' Ba A Kano

Abba Gida-Gida: Ba Za Mu Sake Yarda Da Wani Zabe Na 'Inconlusive' Ba A Kano

  • Injiniya Abba Kabir Yusuf, dan takarar gwamna na NNPP a Kano ya ce jam'iyyarsa da magoya bayansa ba za su amince da 'inconclusive' ba a 2023
  • Abba Gida-Gida, kamar yadda aka saba kiransa ya furta hakan ne yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi ta bakin kakakinsa Sanusi Dawakin-Tofa
  • Abba Yusuf ya ce za su mayar da hankali wurin tattauna batutuwa masu muhimmanci da za su kawo cigaban kasa yayin kamfen ba zagi ba da bita-da-kulli

Kano - Dan takarar gwamnan Kano na jam'iyyar NNPP mai kayan marmari, Injiniya Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da Abba Gida-Gida ya ce jam'iyyarsa da magoya baya ba za su lamunci wani zaben da za a ce bai kammalu ba 'inconclusive' a zaben gwamna na 2023, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yakasai: Ba Zan Iya Muzanta Ganduje Ba Duk Da Ya Kwace Mukamin Da Ya Bani

Taswirar Jihar Kano
Abba Gida-Gida - Ba Za Mu Sake Yarda Da Wani Zabe Na 'Inconlusive' Ba A Kano. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Yusuf ya ce sun shirya tsaf don tunkarar zaben da ke tafe kuma sun dukufa wurin yin kamfen na tattauna batutuwa masu muhimmanci ba bita da kulli da zagi ba don kada a dumama siyasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da ya ke magana da manema labarai a Kano ta bakin kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, dan takarar na NNPP ya ce akasin abin da ya faru a 2019, wannan karon ba za su amince da wani barazana ba kuma za su tabbatar an kirga kuri'unsu don kaucewa wani 'inconclusive'.

Ya ce karuwar masu rajistan zabe a Kano da habbasa da mutane ke yi na tabbatarwa sun yi zabe, suna fatan abin da mutane suka zaba shi zai yi tasiri.

Kalamansa:

"Wannan karon, ba za mu yarda da wani barazana daga kowanne bangare ba a yayin da za mu kasance masu biyayya ga tsarin demokradiyya da bin dokar zabe ta 2022, da aka yi wa kwaskwarima da kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya.

Kara karanta wannan

Rikici: Tashin hankali yayin da kanin miji ya kwace wa dan uwansa mata mai 'ya'ya 7

"Mai girma ya yi farin ciki da juriya, jajircewa da cigaba da goyon baya da masoyansa da mutane Kano ke yi tun farkon takararsa a shekarar 2019."

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel