Jam’iyyu Sun Tona 'Kullaliyar' da Ake Yi Na Canza Shugaban INEC da Birkita Zaben 2023

Jam’iyyu Sun Tona 'Kullaliyar' da Ake Yi Na Canza Shugaban INEC da Birkita Zaben 2023

  • Kungiyoyi kimanin 50 masu zaman kansu da Jam’iyyun adawa sun ce ana shirin batawa Hukumar INEC tsari
  • A wani taron manema labarai da aka yi, shugaban CUPP yace ana so a fasa amfani da na’urar BVAS a 2023
  • Ikenga Imo Ugochinyere ya yi ikirarin ana neman sauke shugaban hukumar INEC saboda ya ki yarda da wannan

Abuja - Jam’iyyun adawa da wasu kungiyoyi masu zaman kansu da jagororin kabilu a Najeriya sun yi ikirarin ana neman kawowa zaben 2023 cikas.

Vanguard a wani rahoto da ta fitar a ranar Larabar nan, tace akwai yunkuri da ake yi na hana tattara kuri’un zaben shugaban kasa da na’urorin zamani.

Masu wannan zargi sun ce sun kuma gano cewa ana neman tursasa hukumar INEC da ta ajiye maganar amfani da na’urar BVAS a gefe a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojin Najeriya sun Kama Wiwi ta N4m wacce Za a Kai wa ‘Yan Ta’adda a Yobe

Kungiyoyin nan sun bayyana wannan ne a lokacin da suka kira taron manema labarai a Abuja.

Rahoton yace wasu gwamnoni na kokarin ganin yadda za suyi domin a canza shugaban hukumar zabe. Farfesa Mahmud Yakubu ne yake rike da INEC.

Shugabannin tsofaffin jam’iyyun da INEC ta sokewa rajista, da kungiyar CUPP da wasu kungiyoyi fiye da 50 masu zaman kansu, suka halarci taron na jiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban INEC
Shugaban Hukumar INEC Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Taron manema labaran ya samu wakilcin jagororin jam’iyyun LP, AA, PDP, ADC da sauransu.

Jawabin Ikenga Imo Ugochinyere bayan taro

Shugaban CUPP, Ikenga Imo Ugochinyere wanda ya karanto jawabi bayan zaman da aka yi, yace wasu sun huro wuta domin a cire BVAS daga garken INEC.

“INEC ta ki yarda da wannan shiri, wannan ya sa ake yunkurin canza shugabannin hukumar zaben,
Wannan zai jawo ayi waje da manyan jami’ai har da shugaban INEC na kasa da wasu daidaikun kwamishononin zabe da suka dage sai an yi amfani da BVAS.”

Kara karanta wannan

Amaechi, da ‘Yan APC 10 da Suka Nemi Takaran 2023, Amma Aka Daina Jin Duriyarsu

- Ikenga Imo Ugochinyere

Shugaban CUPP yace za su garzaya kotu

Punch tace Ikenga Imo Ugochinyere ya yi alwashin za su je kotu domin tilasta amfani da na’urar BVAS wajen gudanar da zaben shugaban kasa da za ayi.

A cewar shugaban na CUPP, karar da za su shigar za ta hana canza shugaban hukumar INEC. Ugochinyere ya zargi gwamnan APC a kudu da wannan shiri.

Satar N1.1bn: Dariye ya yi bayani

An ji tsohon Gwamnan Filato da ya fito daga gidan yari, yayi bayanin yadda aka batar da N1.126bn daga asusun jiharsa, wanda hakan ya yi sanadiyyar daure shi.

Sanata Joshua Dariye yace N100m a cikin kudin sun shiga asusun tazarcen Olusegun Obasanjo a 2003, sannan ya rabawa jam'iyyar PDP fiye da N160m daga kudin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel