Peter Obi: Daga Fitar da Sunayen ‘Yan Kwamitin Zabe, An Fara Rigima a Jam’iyyar LP

Peter Obi: Daga Fitar da Sunayen ‘Yan Kwamitin Zabe, An Fara Rigima a Jam’iyyar LP

  • Dr. Doyin Okupe ya fitar da sunayen mutane fiye da 1200 da za suyi wa Jam’iyyar LP aikin yakin neman zabe
  • Sakataren yada labarai na LP, Arabambi Abayomi ya nuna bai san da batun ba, yace yau za ayi taron NWC

Abuja - Ana zargin wani sabon rikici ya bijirowa jam’iyyar hamayya ta Labour Party da kuma kwamitin yakin neman zaben Peter Obi a zabe mai zuwa.

Vanguard tace rigimar ta kunno kai ne bayan jam’iyya ta fitar da sunayen wadanda za suyi mata yakin neman shugabancin Najeriya da za a gudanar.

Doyin Okupe da ‘yan kwamitinsa na takarar Peter Obi a zaben shugaban kasa sun fitar da sunayen ‘yan kwamitin kamfe ba tare da sanin jam’iyyar LP ba.

Kamar yadda jaridar ta fitar da rahoto a ranar Laraba, sakatariyar LP da ke Abuja ta nuna ba ta san da zaman aikin da su Dr. Doyin Okupe suka gudanar ba.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar LP Ta Fitar Sunayen Mambobi 1,234 Na Tawagar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa, Babu Jiga-Jigai 2

Shugabannin jam’iyyar hamayyar sun ce babu hannunsu a cikin maganar fito da ‘yan kwamitin kamfe, kuma ba su amince da shirin yakin neman zaben ba.

Wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar ta LP da suka yi magana a boye, sun tabbatar da cewa ana kokarin dinke barakar, suka tabbatar da cewa ba da su aka yi aikin ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Peter Obi
Peter Obi a taron ICAN Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

An danne Arewa a yakin zaben

“Mafi yawanmu muna da ra’ayin cewa dole ne kwamitin kamfenmu ya tafi da kowa, ya dauko mutane daga fadin kasar nan.
Bai kamata mu maimaita kuskuren jam’iyyun siyasar da muke neman canzawa ba.
‘Dan takararmu daga Kudu ya fito, Darekta Janar na kamfe shi ma daga Kudu yake. A jerin da na gani, an yi watsi da jihohin Arewa.
Alal misali, babu wasu manyan ‘yan siyasa da aka dauko daga Arewa maso gabas, Arewa maso yamma da Arewa maso tsakiya.”

Kara karanta wannan

Hankalin Iyaye Ya Tashi Bayan Ganin Daliban da Aka Dauke Sun Rike AK47 a Bidiyo

Har a bangaren kwamitin wadanda ke zama kasar waje, an fifita wani bangare a kan wani bangare. Ana tsoron hakan zai iya kawowa LP cikas a filin zabe.

Dr. Okupe sun yi gaggawa?

Okupe ya kira taron manema labarai a jiya a wani dakin taro na Chelsea Hotel da ke garin Abuja.

A wajen aka shirya jagoran na tafiyar Peter Obi zai fitar da sunayen wadanda za suyi aikin kamfe, Emeka Edmond Onwuocha ne ya sa hannu a madadinsa.

Rikicin Atiku da su Wike

A gefe guda, an ji labari ‘Dan takaran PDP, Atiku Abubakar ya jawo mutanen da za su shawo masa kan Gwamnan Ribas, Nyesom Wike da ‘yan bangarensa.

Rigimar da ake yi ta jawo an dakatar da kamfe, an tada tawagar Peter Odili da wasu mutum biyu su dinke barakar jam’iyyar hamayya kafin a shiga filin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel