Atiku Abubakar Ya Kinkimo Manya 3 Domin Su Lallabi Wike Ya Marawa PDP baya

Atiku Abubakar Ya Kinkimo Manya 3 Domin Su Lallabi Wike Ya Marawa PDP baya

  • Atiku Abubakar ya hada tawaga ta musamman da za tayi masa aikin lallashin Gwamna Nyesom Wike
  • James Ibori da Sanata David Mark suna cikin wadanda ake tunanin za su iya shawo kan bangaren Wike
  • Zuwa yanzu jam’iyyar PDP ta tsaida yawon yakin neman zaben shugaban kasa cak saboda rigimar gida

Abuja - Tsohon shugaban majalisar dattawan kasar nan, David Mark yana cikin wadanda jam’iyyar PDP take so su zauna da Gwamna Nyesom Wike.

The Nation tace Atiku Abubakar mai neman zama shugaban kasa a jam’iyyar PDP, ya hada wasu mutum uku da yake sa ran su dinke barakar da ke cikin PDP.

Baya ga Sanata Mark, ana sa ran James Ibori da Peter Odili za su zauna da Gwamnan jihar Ribas domin karkato da ra’ayinsa kan goyon bayan Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

An Samu Sabon Cigaba da Rikicin Atiku da Gwamna Wike, Jam'iyyar PDP Ta Ɗage Yakin Neman Zaɓe

Jam’iyyar hamayyar ta dauki wannan matsaya ne bayan Wike da mutanensa sun kauracewa yawon yakin takarar da Atiku ya fara domin neman mulki.

James Ibori ya yi gwamna a jihar Delta tsakanin 1999 da 2007, kuma bayan ya bar ofis ya cigaba tasiri a jam’iyyar PDP a yankin Kudu maso kudancin kasar.

Haka zalika Peter Odili ya yi gwamna na shekara takwas a jihar Ribas. Odili yana da kyakkyawar alaka da Gwamna Wike, kuma yana da ta-cewa a Neja-Delta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Atiku Abubakar
'Yan kwamitin BOT a gidan Atiku Abubakar Hoto: @Atikuorg
Asali: Facebook

Shi ma Mark wanda ya dade a matsayin na uku a Najeriya, ya yi gwamna a lokacin mulkin Soja, tsohon Sanatan kasar ya fito daga yankin shugaban PDP na kasa.

Tsohon mataimakin shugaban kasar kuma ‘dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa, yana sa ran Wike ya saurari wadannan manyan jam’iyya, ya bi bayansa.

Kara karanta wannan

Akwai Adalci a PDP Sabanin APC: Gwamna Tambuwal Ya Bayyana Bambancin Manyan Jam’iyyun Siyasar Kasar 2

Dole sai an tsige Iyorchia Ayu

Wasu majiyoyi a PDP sun ce sabanin Atiku da wadanda ba su tare da Iyorchia Ayu ne ya jawo aka dakatar da yakin neman zaben shugaban kasa da aka fara.

Kamar yadda wani babba a PDP ya fadawa jaridar, an dauki wannan matsaya ne domin shawo kan wadanda suka dage sai an tunbuke shugaban jam’iyya.

A dalilin haka PDP ta fasa yin gangamin siyasarta a Kebbi. Kola Ologbondiyan yace babu maganar kamfe a jihohin da aka tsara sai zuwa mako mai zuwa.

Za ayi kamfe ko babu su Wike

A baya an samu rahoto cewa 'dan takarar shugaban ƙasar na PDP watau Atiku Abubakar, ya zabi ya cigaba da kamfe ba tare da bangaren su Wike ba.

Kuna sane cewa Gwamnan na Ribas da su Samuel Ortom, Seyi Makinde, Ifeanyi Ugwuanyi da Okezie Ikpeazu sun zabi su ki goyon bayan ‘dan takaransu.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike da Wasu Kusoshi da Suka Ki Halartar Taron Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel