Sanata Ya Gargadi PDP KarTa Yi Kuskuren Watsi da Wike, da Wasu Gwamnoni 4

Sanata Ya Gargadi PDP KarTa Yi Kuskuren Watsi da Wike, da Wasu Gwamnoni 4

  • Sanata Chimaroke Nnamani, ya gargaɗi shugabannin PDP kada su tafka kuskuren watsi da gwamnoni biyar da suka fusata
  • Tsohon gwamnan jihar Enugu yace gwamna Wike da takwarorinsa huɗu da suka kauracewa taron PDP sun fi karfin a jingine su
  • Har yanzun dai ana kai ruwa rana tsakanin shugabancin PDP na ƙasa da tsagin gwamna Wike na Ribas

Enugu - Sanata mai wakiltar mazaɓar Enugu ta gabas, Chimaroke Nnamani, ya ayyana rashin halartar gwamnonin PDP masu ci 5 wurin buɗe babin kamfen shugaban kasa da koma baya mai kashe kwarin guiwa.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa jam'iyyar PDP ta bude yaƙin neman zaɓen shugaban kasa ranar Litinin a Uyo, babban birnin Akwa Ibom.

Sanata Chimaroke Nnamani.
Sanata Ya Gargadi PDP KarTa Yi Kuskuren Watsi da Wike, da Wasu Gwamnoni 4 Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Sai dai gwamna Wike da wasu makusantansa, Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom, gwamnan Abiya, Okezie Ikpeazu da gwamnan Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, ba su halarci wurin ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike da Wasu Kusoshi da Suka Ki Halartar Taron Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na PDP

Sanata Nnamani ya gargaɗi uwar jam'iyya ta ƙasa kar ta tafka kuskuren jingine gwamna Nyesom Wike na Ribas da takwarorinsa huɗu waɗanda suka nuna fushi saboda yin haka ka iya nakasa PDP a zaɓen 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nnamani, tsohon gwamna na tsawon zango biyu daga 1999 zuwa 2007 a jihar Enugu, ya yi wannan gargaɗin ne a wata sanarwa da ya rattaba wa hannu kuma ta fita a Abuja ranar Talata.

Ya bayyan cewa, "Babban girman kai ne," ga shugabannin jam'iyya na ƙasa su yanke banzatar da tawaga mai matuƙar muhimmanci da ta kunshi gwamnoni 5 dake kan madafun iko.

Sanatan yace:

"A yau ina Alla-wadai da yadda ake wa gwamnoni biyar a cikin jam'iyyar PDP mafi yawansu daga kudancin Najeriya. Gwamnoni sune jagororin mu kuma wulaƙanta su zai shafe mu baki ɗaya."

Kara karanta wannan

2023: Ana Shirin Bude Kamfe Yau, Atiku Ya Dauki Matakin Karshe Kan Rikicinsa da Gwamna Wike

Ya Kamata PDP ta yi karatun ta nutsu - Nnamani

Bugu da ƙari ya haƙaito cewa ba haka ake wa gwamnonin jihohi ba a lokacin yana kan kujerar gwamna. Bisa haka ya kara gargaɗin jam'iyyar kan darewar PDP a jihohin da lamarin nan ya shafa.

"Daga tushe ake ɗakko siyasa kuma waɗannan 'yan koren dake ɗasawa da shugabannin PDP ba zasu iya kai labari a runfunansu ba idan gwamnoni ba su tallafa ba."
"Ba tare da sa hannun gwamnoni ba waɗan nan da kuke gani ba zasu kai labari ba. Zasu wanke kafa ne kawai daga gida zuwa Abuja, wasu ma can suka koma da zama."

A wani labarin kuma mun kawo muku Kalaman da Tinubu Ya Nemi Tawagar Matan APC Su Faɗa Wa Yan Najeriya Masu Neman Canji a 2023

Ɗan takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya nemi matan APC su gaya wa masu neman canjin gwamnati su yi wa mutane shiru.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Fitaccen Dan Siyasa Kuma Na Kusa da Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Rasu

Tsohon gwamnan jihar Legas ɗin yace jam'iyyar APC ta hau gadon mulki lokacin da ƙasar nan ke cikin yanayi mai muni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel