Rikicin PDP: Atiku Ya Kama Harkokin Gabansa Ba Tare da Wike Ba, Majiyar PCC

Rikicin PDP: Atiku Ya Kama Harkokin Gabansa Ba Tare da Wike Ba, Majiyar PCC

  • Wasu bayanai sun nuna cewa dan takarar shugaban ƙasa a PDP, Atiku Abubakar, ya yanke ci gaba da kamfe ko babu su gwamna Wike
  • Atiku da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, sun samu saɓani kan bukatar sauke shugaban PDP na kasa daga muƙaminsa
  • A yau Litinin, jam'iyyar PDP zata buɗe babin yakin neman zaben shugaban kasa a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom

Abuja - A yau Litinin 10 ga watan Oktoba, 2022, babbar jam'iyyar hamayya PDP zata buɗe yaƙin neman zaben shugaban ƙasa a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.

Jaridar Vanguard ta gano cewa da yuwuwar dan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya yanke hukuncin fuskantar abinda ke gabansa da Wike ko babu shi.

Wasu bayanai daga wani na ƙusa da Atiku sun nuna cewa mafi yawan mambobin jam'iyya sun yi watsi da kiraye-kirayen da gwamna Wike na Ribas da yan tawagar ke yi na shugaban PDP, Iyorchia Ayu, ya yi murabus.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike da Wasu Kusoshi da Suka Ki Halartar Taron Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na PDP

Gwamna Wike da Atiku Abubakar.
Rikicin PDP: Atiku Ya Kama Harkokin Gabansa Ba Tare da Wike Ba, Majiyar PCC Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

Bugu da ƙari, jagoran tafiyar Ward2Ward4Atiku, Abraham Chila, ƙungiyar da ke kokarin tattara wa Atiku mutane tun daga tushe, yace arewa ta tsakiya ba zata yarda a sauke Ayu ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, shugaban PDP na ƙasa ba zai sadaukar da kujerarsa ba kamar yadda Chief Audu Ogbeh, ya yi lokacin da aka tilasta masa sauka daga jagorancin PDP a baya.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa hakan ya biyo bayan ƙarin bayanan da ake samu kan yadda mambobin kwamitin ayyuka (NWC) da ma'aikata suka yi kashe mu raba na biliyan N1.3bn alawus ɗin gida.

Atiku da Wike sun jima ba su ga maciji kan bukatar sauke Ayu daga mukaminsa. Hakan yasa wasu kusoshin PDP suka tsame hannu daga tawagar Kamfe kan ƙin saukar Ayu.

Wane mataki Atiku ya ɗauka?

Wata majiya ta shaida wa Vanguard cewa Atiku da makusantansa sun yanke ci gaba da harkokin kamfe ba tare da gwamna Wike da sauran masu mara masa baya ba.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Mummunan Hari, Sun Kashe Mai Anguwa da Wasu Mutune a Jihar Arewa

Majiyar, wanda makusanci ne ga tsohon mataimakin shugaban ƙasan yace:

"Bari na faɗa muku wata gaskiya, game da yadda batun Wike ke tafiya, akwai kwarin guiwar cewa za'a ci gaba da kamfe. Saboda haka idan Wike ko wani ɗan tsagin ya nuna sha'awar shigowa a dama da shi, muna maraba."
"Amma ba wanda ke jiransu a yanzu saboda ba su da wani abu da zasu iya don dakatar da shirin. Wannan shi ne abinda kowa ke ganin ya dace."

Shin bukatar Ayu ya yi murabus zata yuwu?

Game da batun Ayu ya yi murabus sannan a naɗa kwamitin riƙon jam'iyya, majiyar ta ƙara da cewa ba zai yuwu ba.

"Abunda suke magana a kai ba abu ne da kowa zai ɗauka dagaske ba, ba zai yuwu a naɗa kwamitin rikon kwarya ba kuma ba wanda zai yarda saboda ya saɓa wa doka."
"Idan ka duba abinda ƙe faruwa a APC, Abu ne da Kotu ke cewa ko dai yan takararsu na kan doka ko sun saɓa wa doka. Yadda NWC yake yanzu haka ya dace a bar shi, idan aka taba shi zai shafi muhimman abubuwa."

Kara karanta wannan

Tinubu, Atiku Ko Kwankwaso? An Bayyana Dan Takarar Da Ya Shirya Ceto Najeriya Idan Ya Gaji Buhari a 2023

A wani labarin kuma Shugaban APC Na Ƙasa Ya Faɗi Babban Abinda Zai Sa Tinubu Ya Sha Kaye a Zaɓen 2023

Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, yace idan har gwamnoni suka zare hannunsu jam'iyyar ba zata kai labari ba a 2023.

Tsohon gwamnan jihar Nasarawa yace nasarar APC na hannun Allah kuma tana hannun gwamnoni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel